Hatsari a ginin tarihi na Chana: Rufin hasumiyar Daular Ming ya faɗi

Spread the love

A lardin Shanxi na ƙasar Chana, wani gini mai tarihi daga zamanin Daular Ming mai kimanin shekaru 650 ya fuskanci hatsari, inda rufin ginin ya faɗo yayin da wasu baƙi ke ziyarta. Bidiyon da aka ɗauka ya nuna yadda katanga da tubalan ginin suka faɗo kusa da jama’ar da ke yawo.

Gwamnatin yankin ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin wannan hatsari, tare da duba irin matakan da ke wajaba a ɗauka wajen kula da gine-ginen tarihi. Masana al’adu da gine-gine sun bayyana damuwar cewa, ana barin gine-ginen tarihi ba tare da kulawa da su yadda ya kamata ba, duk kuwa da biliyoyin yuan da aka ware a kasafin kuɗin ƙasar domin adana su.

By ukarofi