Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT Global), wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta ƙasa da ƙasa mai matsayin tuntuɓa na musamman a Majalisar Tattalin Arziki da Zamantakewa ta Majalisar ɗinkin Duniya (UN ECOSOC), ta bayyana jin daɗinta kan sanarwar da Gwamnatin Jihar Filato ta fitar dangane da hukuncin da Babbar Kotun Jihar Filato ta yanke kan rikicin da ya shafi ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.
A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta ce tana yaba wa Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Manasseh Mutfwang, saboda jaddada muhimmancin bin doka da oda, mutunta ’yancin kai na ɓangaren shari’a, tabbatar da adalci ta hanyar bin ƙa’idojin doka, da kuma kare haƙƙoƙi da martabar dukkan mazauna jihar ba tare da la’akari da bambancin ƙabila, addini ko al’ada ba.
Sanarwar ta samu sa hannun Abdullahi Bakoji Adamu, Daraktan ƙasa na Nijeriya na ƙunhiyar Kare Haƙƙin ɗan Adam ta Duniya (IHRC-RFT Global).
IHRC-RFT ta kuma yi maraba da kiran da gwamnan ya yi na a kwantar da hankula, a mutunta tsarin shari’a, tare da kauce wa duk wani mataki ko furuci da zai iya haddasa rabuwar kai ko kawo barazana ga zaman lafiya. ƙungiyar ta bayyana cewa waɗannan ɗabi’u sun yi daidai da ginshiƙƙn dimokuraɗiyya da kuma ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan Adam da duniya ta amince da su.
Sai dai kuma, a cikin wannan yanayi na mutunta kundin tsarin mulki da kare haƙƙin ɗan Adam, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta sake duba tare da janye duk wata sanarwa ko umarni da ke nuna cewa ya kamata a harbe makiyayan da aka samu suna kiwo a gonaki.
ƙungiyar ta bayyana cewa duk da cikakken goyon bayan da take bai wa matakan kare manoma, gonakinsu da kadarorin al’umma daga kutse ba bisa ƙa’ida ba, amfani da ƙarfi mai kashe rai ba tare da bin cikakken tsarin doka ba na haifar da damuwa mai girma dangane da haƙƙin rayuwa, bin ƙa’idojin shari’a da kuma mutunta Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya.
A cewar ƙungiyar, laifuffukan da suka shafi karya dokokin amfani da ƙasa, dokokin hana kiwo a fili ko wasu laifuka makamantansu ya kamata a magance su ta hanyoyin doka kamar kama wanda ake zargi, gudanar da bincike, gurfanar da shi a gaban kotu da kuma bari kotu ta yanke hukunci, maimakon ɗaukar matakan da za su iya zama kamar amincewa da hukunci ba tare da bin doka ba.
IHRC-RFT ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta zaman lafiya, adalci, tattaunawa da zaman tare cikin jituwa tsakanin al’ummomi a Jihar Filato da ma Nijeriya baki ɗaya.
ƙungiyar ta bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kare ƙa’idojin kundin tsarin mulki, mutunta haƙƙoƙin ɗan Adam da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga cibiyoyin dimokuraɗiyya.
