Ina son barin Atletico Madrid, inji Alvarez

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan wasan gaba na ƙasar Argentina, Julian Alvarez ya tabbatar da aniyarsa ta ficewa daga ƙungiyar Atletico Madrid, lamarin da ke ƙara wa raɗe-raɗin babbar hada-hadar sauya sheƙa akan ɗan wasan.

Alvarez ya furta haka ne a wata hira da ESPN bayan wasan da Argentina ta doke Austria da ci 2 da nema a gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana.

A cewarsa, tuni ya fara tattaunawa da jami’an Atletico kuma yana ganin sauya sheƙa a yanzu shi ne abin da ya fi dacewa a gare shi da ƙungiyar.

Haka kuma, ɗan wasan mai shekaru 26 bai bayyana haƙiƙanin ƙungiyar da yake fatan koma wa ba, amma kalamansu sun nuna cewa yana fatan samun tayi daga manyan ƙungiyoyin Nahiyar Turai.

Rahotanni sun bayyana cewa, daga cikin ƙungiyoyin da ke kwaɗayin siyan ɗan wasan akwai Real Madrid, Arsenal da kuma Barcelona.

By Babaji

Leave a Reply