Kamfanonin ƙasar Sin sun bada kyauta ga ɗaliban Ghana da ke fama da talauci

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Wasu kamfanoni biyu na ƙasar Sin, sun baiwa wasu ɗaliban makarantun firamare dake ƙasar Ghana kyauta, albarkacin bikin ranar yara ta duniya da aka shirya a birnin Jamestown, daya daga cikin al’ummomin da ke fama da talauci a Accra, babban birnin ƙasar Ghana.

Kamfanin CRCC Harbor da kamfanin CCCC First Harbor Consultants CO., LTD, sun ba da gudummawar gwomman kwallayen kafa, da jakunkuna na makaranta, da fensira masu launi, da abin goge rubuta, da sauran kayan makaranta masu yawa ga makarantar reno ta Chirst the king of kings, wadda ke kusa da tashar kamun kifi ta Jamestown da ƙasar Sin ta samar wanda kamfanonin biyu suka gina.

Shugaban makarantar Paul Yaw Owusu, ya yaba wa manyan kamfanonin ƙasar Sin da taimakon da suka baiwa makarantar ta hanyoyi daban-daban, kama daga bayar da gudumawa zuwa aikin tsaftace muhalli.

Ya bayyana cewa, ilimi shi ne mabudin samun nasara, kuma an san cewa, kayayyakin da kamfanonin suka samar, za su taimakawa yaran matuka a ƙoƙarinsu na samun ilimi, don zama abin da suke so su zama a nan gaba.

Fassarawa: Ibrahim Yaya

By Editor