Ya kamata Sin da Amurka su samar da kyakkawan yanayin yin haɗin gwiwa tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar kasuwancin ƙasar Sin Gao Feng, ya bayyana a yau Alhamis cewa, har kullum ƙasar Sin na adawa da sanya takunkumi don ƙashin kai, da ɗaukar matakai kan wasu ƙasashe bisa dokokin ƙasar Amurka, kuma kamata ya yi Sin da Amurka su ɗauki matakai bisa buri iri ɗaya, a ƙoƙarin samar da kyakkyawan yanayi, da sharuɗɗan na yin haɗin gwiwa a tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

Dangane da ra’ayin wasu jami’an Amurka, kan sanya takunkumi ga kayayyakin da kamfanonin ƙasar Sin suke sayarwa Amurka, Gao Feng ya nuna cewa, ƙasar Sin ba za ta amince da matakin ba.

Kakakin ya ƙara da cewa, a kwanan baya, gwamnatin Amurka ta yi nazarci batun soke ƙarin haraji da ta dora kan kayayyakin ƙasar Sin, lamarin da ya dace da muradun masana’antun Sin da Amurka, da muraddun Amurkawa masu sayayya, da ma muraddun ƙasashen duniya baki ɗayan. Ya ce kamata ya yi Sin da Amurka su ɗauki matakai bisa buri iri ɗaya, a ƙoƙarin samar da kyakkyawan yanayi da sharuɗɗan na yin hadin gwiwa a tsakaninsu, ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da ƙara samarwa al’ummun ƙasashen 2 alherai.

Fassarawa: Tasallah Yuan

By Editor