Kashe-kashe: Shugaban Sojoji ya tare a Benue

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban Sojojin Nijeriya (COAS), Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya yi ƙaura zuwa Makurďi, Babban Birnin Jihar Benue a sakamakon aukuwar yawan kashe-kashen ƴan ƙauye da makiyaya da ƴan bindiga suke yi a jihar.

Lamarin ya yi sanadin rasa rayuka da dama da raunata wasu gami da ƙone gidaje, wanda hakan ya ɗaiɗaita mutane da dama.

A safiyar ranar Talata ne Laftanal Janar Oluyede ya bar Abuja tare da wasu manyan jami’ai (PSOs) daga ofishinsa da wasu daga Hedikwatar Tsaro zuwa jihar da nufin ganin halin da ake ciki game da al’amarin.

Babban jami’in zai gana ne da kwamandodin sojoji a jihar domin samar da hanyoyin kawo ƙarshen kashe-kashen.

Haka kuma, zai ziyarci sansanonin sojoji da wuraren atisaye, inda zai gana da jami’an kai-tsaye domin ƙarfafa musu a ƙoƙarinsu na tabbatar da tsaro.

Bugu da ƙari, Oluyede zai kai ziyara ƙauyukan da aka kai musu hare-hare gami da ba su tabbacin bada kariya ga rayukansu da dukiyoyinsu.

By Babaji