Mara wa kamfanoni ma su zaman kansu baya zai amfani ƙasar Sin da ma duniya baki ɗaya

Daga CMG Hausa

Kwanan baya shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadin aiki a lardin Sichuan dake yammacin ƙasar Sin, inda ya ziyarci wani kamfani mai zaman kansa mai suna Gimi, dake ƙera kayan laturoni, da na samar da wutar lantarki.

Shugaba Xi ya shiga ɗakin nune-nune da sashin ƙere-ƙere na kamfanin, inda ya ƙara fahimtar yadda kamfanin ke gudanar da ayyukan ƙirƙire-ƙirƙire da nuna goyon-baya ga raya tattalin arzikin wurin da sauransu, al’amarin da ya sake shaida cewa, ƙasar Sin na matukar maida hankali, gami da nuna goyon-baya ga raya tattalin arziki mai zaman kansa.

Sakamakon yaɗuwar annobar COVID-19, da sauye-sauyen halin da ake ciki na gida da waje, da rashin sanin tabbas, kamfanoni masu zaman kansu na ƙara fuskantar kalubaloli, inda gwamnatoci a matakai daban-daban na ƙasar Sin ke lalibo hanyoyi daban-daban da tallafa musu don haye wahalhalu da samar da ci gaba. A yayin ziyarar shugaba Xi a wannan karo, ya ganewa idanunsa manufofin gwamnatin wurin na taimakawa kamfanonin dake fuskantar matsala.

To shin ko ina mafita ga kamfanoni masu zaman kansu, don samun sabbin damammaki a yayin da suke fuskantar matsaloli da sauye-sauye? Amsar nan ita ce, yin ƙirƙire-ƙirƙire.

Kamfanin Gimi da shugaba Xi ya ziyarta a wannan karo, kamfani ne dake kan gaba a ƙasar Sin a ɓangaren samar da na’urorin ƙera allon majigi, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, ya dace a inganta ƙarfin yin ƙirƙire-ƙirƙire, da gaggauta raya ƙasar Sin har ta zama ƙasa mai karfin ƙere-ƙere. Kalaman Xi sun ƙarfafa gwiwar kamfanoni masu zaman kansu na ƙasar Sin, don shawo kan ƙalubaloli da samar da ci gaba, kana, za su kara taimakawa wajen farfaɗo da tattalin arzikin duniya.

Fassarawa: Murtala Zhang