Jakadan Sin a Saliyo ya halarci taron ƙarawa juna sani tsakanin ofishin jakadancinsa da ƙungiyoyin sada zumunta ta ƙasashen biyu

Daga CMG HAUSA

A ranar 8 ga wata, ofishin jakadancin ƙasar Sin dake Saliyo, ya shirya taron ƙarawa juna sani tsakanin ofishin da ƙungiyoyin sada zumunta ta ƙasashen Sin da Saliyo na shekarar 2022.

Jakadan ƙasar Sin a Saliyo, Hu Zhangliang, ya gabatar da muhimmin jawabi game da halin da ƙasa da ƙasa ke ciki a halin yanzu, da manufofin bunƙasa cigaba na ƙasar Sin da na diflomasiyyarta, da kuma hulɗar dake tsakanin Sin da Saliyo. Ya bayyana cewa, ƙasar Sin ta ƙara ƙaimi tare da samar da gagarumin taimako ga zaman lafiya da cigaban duniya. Yadda ƙasar da ke da al’umma biliyan 1.4 ta bunƙasa, wani babban cigaba ne ga bil adama baki ɗaya, ba wai barazana ce ko kuma ƙalubale ga duniya ba.

Jakada Hu, ya bayyana cewa, duk wani yunkurin bata sunan ƙasar Sin, da neman lalata hulɗar dake tsakanin Sin da Saliyo da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika ba zai taba samun karɓuwa ba. Kasar Sin a shirye take ta cigaba da ƙarfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakaninta da ƙasar Saliyo, domin amfanawa ɓangarorin biyu.

Shugabannin ƙungiyoyin sada zumunci tsakanin Saliyo da Sin, da wakilan kafafen yaɗa labaran ƙasar ta Saliyo sun bayyana cewa, ƙasar Sin ta samar da taimako na gaskiya don cigaban ƙasashen Afrika, cikinsu har da ƙasar Saliyo, a dogon lokaci, kana zumuncin dake tsakanin Sin da Saliyo, da kuma na Sin da Afrika, ya yi matuƙar ratsa zukatan al’umma. Duk wani yunƙurin neman lalata kimar kasar Sin, da neman lalata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Saliyo ba zai taɓa samun nasara ba.

Fassarawa: Ahmad