Me aka tattauna a wajen shawarwarin ministocin tsaron Sin da Amurka?

Daga CMG HAUSA

Jiya Jumma’a 10 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron ƙasar Sin, Wu Qian, ya kira taron manema labarai a wajen shawarwarin Shangri-La ko kuma SLD a taƙaice a ƙasar Singapore, inda ya bayyana yadda aka gudanar da shawarwarin ministocin tsaron ƙasashen Sin da Amurka. Wu ya ce, a yayin shawarwarin, ministan tsaron ƙasar Sin, Wei Fenghe, ya jaddada matsayin ƙasar Sin kan batun Taiwan, inda ya ce, Sin ƙasa ce daya tilo a duniya, kuma Taiwan wani yanki ne da ba za’a iya balle shi daga ƙasar Sin ba. Manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tilo a duniya, tushen siyasa ne na alaƙoƙin Sin da Amurka, kana, amfani da batun Taiwan don kawo cikas ga ci gaban ƙasar Sin ba zai kai ga nasara ba.

Minista Wei ya ce, kwanan baya, ƙasar Amurka ta sake sanar da cewa za ta sayar da makamai ga yankin Taiwan, al’amarin da ya sabawa manufar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya, gami da ƙa’idojin sanarwar hadin-gwiwa uku na kasashen biyu, da lalata cikakken yankin ƙasar Sin da moriyar tsaronta, kana lamarin ya lalata dangantakar Sin da Amurka da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. Ƙasar Sin ta nuna adawa gami da yin Allah wadai da irin wannan batu.

Wu Qian ya ce, minista Wei ya jaddada cewa, in dai akwai wanda ke yunkurin balle Taiwan daga ƙasar Sin, babu tantama rundunar sojan ƙasar Sin za ta mayar da martani don tona asirinsu, da kiyaye cikakken yankin na ƙasar Sin.

Wu Qian ya ƙara da cewa, dangane da batun tekun kudancin ƙasar Sin, minista Wei ya ce, ƙasashen dake wannan yankin, suna da niyya da hikima gami da kwarewa sosai wajen daidaita batutuwan da suka shafi tekun kudancin ƙasar Sin. Shisshigin da ƙasashen da ba na wannan yanki ba suka yi, shi ne ke kawo rashin tabbas. Ya dace ƙasar Amurka ta ɗauki matakai a zahiri don amfanawa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin ƙasar Sin, maimakon rura wutar rikici da tunzurin neman haifar da fito-na-fito.

An ƙaddamar da shawarwarin Shangri-La (SLD) karo na 19 a ƙasar Singapore a jiya Jumma’a, inda memban majalisar gudanarwa na ƙasar Sin, wanda kuma shi ne ministan tsaron ƙasar, Wei Fenghe ya halarci shawarwarin, da halartar tattaunawa da takwaransa na Amurka, Lloyd Austin. (Murtala Zhang)