Miyetti Allah da CAN sun nuna damuwarsu kan harin Jos

Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), ta yi tir da harin da aka kai wa al’ummar hanyar Rukuba da ke Jos, Jihar Filato.

Haka nan, ƙungiyar ta buƙaci jami’an tsaro da su dukufa bincike don gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki don su fuskanci hukunci.

MACBAN ta yi waɗannan bayanan ne cikin sanarwar da ta fitar ta hannun sakatarenta na ƙasa, Baba Othman Ngelzarma, a Jos a ranar Lahadi.

Ƙungiyar ta nuna damuwarta kan yadda
har yanzu ba a gano wasu mazauna yankin ba kimanin su 40 da suka ɓata sakamakon harin.

Yayin da ta yi amfani da wannan dama wajen jajanta wa ‘yan’uwan waɗanda harin ya rutsa da su, haka nan ƙungiyar ta ce wajibi ne a lalubo hanyoyin da za su taimaka wajen hana ci gaba da zubar da jinin mutane.

A hannu guda, ita ma Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN) reshen Jihar Filato, ta fito ta nuna damuwarta kan wannan mummunan al’amari da ya auku.

Cikin sanarwar da CAN ɗin ta fitar a Lahadi a Jos, shugabanta na jihar,  Rev. Fr. Polycarp Lubo, ya yi kira ga jami’an tsaro da su binciko ɓatagarin da suka yi wannan aika-aikar.

Lubo ya sake yin tir da yadda ake ci gaba da kashe mutane a yankunan Bassa da Riyom da Jos ta Kudu da kuma yankin ƙaramar hukumar Barkin Ladi.

Ya ce ran kowane mahaluki abu ne mai daraja, don haka ya ce ba daidai ba ne yadda ake ta kashe mutane a sassa.

Daga nan, Lubo ya jajanta wa ‘yan’uwan duka waɗanda harin ya rutsa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *