Gerd Muller ya kwanta dama

Tsohon zakaran ƙwallon ƙafar ƙasar Jus, Gerd Muller, ya rasu. Muller ya bar duniya yana da sheka 75.

Bayanai sun nuna a halin rayuwarsa, Muller ya kasance ɗan wasan da ya fi kowa zira ƙwallaye a Bayern Munich inda ya ci ƙwallaye guda 563 a wasanni 605 na Bundesliga,

Tun a 2015 aka gano marigayin na ɗauke da cutar Alzheimer, lokacin da yake kocin ƙungiya ta biyu ta Bayern.

A wani sako da ta wallafa a shafinta ma Tiwita, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta ce, “Yau duniyar FC Bayern ta tsaya cak. Gwarzon ɗan wasan Jamus da dukkan magoya bayansa sun yi jimami tare da makokin mutuwar Gerd Müller, wanda ya mutu da sanyin safiyar Lahadi yana ɗan shekara 75.”

Da yake magana game da rasuwar Muller, shugaban Bayern, Herbert Hainer, ya ce, “Yau rana ce ta bakin ciki ga FC Bayern da dukkan magoya bayanta. Gerd Müller shi ne babban ɗan wasan da aka taɓa samu – kuma mutum ne mai hazaƙa fahen ƙwallon ƙafa na duniya.”

Ya ci gaba da cewa, “Za mu kasance cikin tsananin baƙin ciki tare da matarsa ​​Uschi da dangins na rashin Gerd Müller….”

Muller

Shi kuwa babban jami’in Bayern, Oliver Kahn, cikin wata sanarwa da ya fitar dangane da rashin ya ce, “Labarin mutuwar Gerd Müller ya shafe mu duka.

“Yana ɗaya daga cikin manyan ababen tunawa a tarihin FC Bayern, nasarorinsa ba su misaltuwa har zuwa yau kuma za su kasance cikin tarihin FC Bayern da na ƙwallon ƙafa ta Jamus.”