Kwamishinan Hukumar Alhazai ya yi auren ɗiya a Kano

Daga AMINA YUSUF ALI a Kano

A yau Lahadi, 15 ga watan Agustan, 2021 ne ɗaruruwan ‘yan’uwa da abokan arziki suka yi dafifi i zuwa masallacin Murtala da ke Jihar Kano domin halartar ɗaurin auren Dakta Hannatu, ɗiya a gurin Alhaji Nura Hussaini Yakasai wanda Kwamishina ne mai kula da tsare-tsare da kuma harkokin Kuɗi a Hukumar Alhazai ta Najeriya. Wadda aka bayar da aurenta ga Arc. Muhammad Shafiq Kamal.

A yayin da yake zantawa da ‘yan jaridu a wajen ɗaurin auren, Alhaji Yakasai ya bayyana irin matsanancin farin cikinsa da Allah ya kawo shi ranar da zai ba da auren ɗiyarsa. Kuma ya ce wannan rana ce mai tarihi a wajensa domin rana ce da ya aurar da ɗiyarsa ta fari.

Alhaji Yakasai ya bayyana cewa, shi yana da yaƙinin cewa, ya yi wa ɗiyarsa ingantacciyar tarbiyya wacce za ta zama mace tagari. Sannan kuma ya ce yana da yaƙinin cewa, shi ma angon mutumin kirki ne wanda zai iya riƙe matarsa bisa amana.

A cewar sa, duka yaran suna da tarbiyya, kuma yana yi musu fatan samun zaman lafiya a auren nasu. Kuma yana musu fatan Allah ya dawwamar musu da farin ciki da rayuwar aure mai ɗorewa. ‘

Sannan kuma ya ƙara da yin kira ga ma’auratan da su tafiyar da rayuwarsu a kan turbar koyarwar Annabi Muhammad (SAW).

Daga ƙarshe, Alhaji Yakasai ya bayyana godiyarsa ga shugaban Hukumar ta Alhazai, (NAHCON) Barista Zikirullah Kunle Hassan, da ma’aikatan dake ƙarƙashinsa na hukumar alhazan, da ma dukkan mutanen da suka samu halartar ɗaurin auren. Inda ya yi musu fatan komawa gidajensu lafiya.

Shi ma a yayin da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban sashen labarai na NAHCON, Muhammad Ahmad Musa, wanda ya taya uban amarya murnar aurar da ‘yarsa da ya yi. Sannan ya yi musu fatan samun albarka mai ɗorewa a auren.

Sannan kuma ya shawarci ma’auratan da su sauke haƙƙoƙin junansu da ya rataya a wuyansu, sannan kuma su tarbiyyantar da yaran da za su haifa bisa doron sunnar Annabi (SAW), domin su amfanar da al’umma.