Na samu Jihar Kano a mawuyacin halin tsaro – CP Sama’ila Dikko

Spread the love

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Dikko, ya bayyana cewa ya samu Jihar Kano cikin mawuyacin halin tsaro, amma zuwan sa sun haɗa kai da masu ruwa da tsaki sun shawo kan lamarin.

Da yake ƙarin haske ga wakilin Manhaja a makon jiya, dangane da yadda ya samu Jihar ta Kano a matsayin Kwamishinan ‘Yan Sanda, ya ce lallai ya samu jihar a wani hali na ƙuncin rashin tsaro ta fuskoki daban-daban, amma kuma bai yi ƙasa a gwuiwa ba wajen zama da sauran jami’an ‘yan sandan da ɓangarorin da ya kamata don ƙara masa haske don fahimtar da tasa wannan matsaloli suka yi shura a jihar da ke kan gaba a Arewa ta fuskar kasuwanci da zaman lafiya.

Kwamishinan ya cigaba da cewa zuwansa ya fahimci Jihar Kano na cikin matsalolin garkuwa da mutane, sara-suka, harkar ƙwacen wayar hannu tare da fashi da makami da sauran wasu matsaloli da yawan gaske, kama daga kayan aiki da suka haɗa da motoci da dukkan wasu na’urorin da ake amfani da su wajen gudanar da aiki sun samu rauni.

Sannan CP ya kuma tabbatar da ziyartar sarakunan Jihar Kano tun farko, musamman mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero a matsayinsa na uba ga kowa a wannan jihar saboda muhimmancinsa da rawar da zai iya takawa ta fuskar wanzar da zaman lafiya a jihar

Bayan wanna ne ma kuma kwamishinan ya ce ya kuma samu damar kai wa maigirma gwamnan jiha Kano ziyara tare da bayyana masa irin dalilan da ya sa Maigirma shugaban rundunar ‘yan sanda na ƙasa ya kawo shi wannan jiha don kawo gyara daga waɗancan matsaloli dake addabar jihar Kano.

By Editor