Za mu ci gaba da kawo sauyi ta fuskar kasuwanci a Jihar Kano – Shugaban Alkamatu

Spread the love

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Shugaban Kamfanin Alkamatu a Jihar Kano, Kwamared Alkamatu Abdulkadir ya ce za su cigaba da kawo sauhe-sauye masu ma’ana ta fuskar kasuwanci a Jihar Kano.

A ci gaba da wayar wa da matasa da al’ummar Jihar Kano da suke yi dangane da muhimmancin dogaro da kai ta fuskar kasuwanci da matakin da ya kamata a ce al’umma sun bi wajen ganin sun zama masu dogaro da kansu da kamfanin Alkamatu ke ta fafutukar yi ga al’ummar jihar Kano, Alkamatu ya buƙaci sahalewar gwamnati da masu hannu da shuni kan ƙara zuwa don zuba hannu jarinsu.

Alkamatu Abdulkadeer ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da bita karo na ɗaya da na biyu wajen ganin jama’a sun ƙara samun haske da fahimtar yadda za su gudanar da kasuwa musamman waɗanda suke neman taimako daga gidaunyar Tony Elumelu da kamfanin Alkamatu Brain Box Solution ke ta fafutikar ganin kowa ya zama miloniya ta fuskar kasuwanci a jihar..

Idan dai ana biye, shugaban kamfanin na Alkamatu yana gabatar da bitar ne a gidan redion zamani na Premier FM a kowace ranar Larabar kowane mako da yanzu an shiga mako na biyu wajen gabatar da shirin bitar kasuwanci, ba ma ga waɗanda suke nema ba, a’a har ma da wanda ba su cikin tafiyar su kan amfana da shirin ta karatun da shugaban da ke “feɗe biri har wutsiya ya yi bitar da za ta ɗauki tsawon sati tara kafin kammalata.

Idan dai ba a manta ba gidauniyar TEF ta samu damar bai wa matasa sama da ɗari da goma tallafin Naira milyan biyu ga kowa a kwanan baya ƙarƙashin wannan kamfani na Alkamatu Brain Box Solution da suke ƙoƙarin ganin an samar wa da matasa hanyar dogaro da kai ba dare ba rana a Jihar Kano da ma sauran jihohi Arewa.

By Editor