Najeriya ce ta 8 a jerin ƙasashen da ake sayar da fetur da arha – Bincike

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai farashin fetur a ƙasashe da dama na Duniya na yin tashin gwauron zabon da bai tava yi ba. Hakan na faruwa ne saboda rashin samun shi a wadace da ba a yi yanzu a Duniya.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, wani sabon rahoto da wani kamfanin binciken ƙwaƙwaf mai suna Zutobi ya fitar, ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta 8 a jerin ƙasashen da har yanzu ake sayen litar fetur arha.

An dai buga wannan bincike a cikin watan Afrilu, inda farashin galan 1 ke daidai da dala 1.82.

Ƙasashen da ke sahun farko a arhar fetur kafin Najeriya sun haɗa da Venezuela, ƙasa mai arzikin fetur dake Kudancin Amurka a matsayin wadda ta fi arhar fetur.

A Venuzuela dai galan 1 na fetur bai kai Naira 60 ba. Ana sayar da galan guda a kan dala 0.11 kacal! Venezuela ce ta fi kowace ƙasa a duniya yawan ɗanyen mai kwance a ƙasa.

Libya ce ƙasa ta biyu wajen arhar fetur. Libya da Venezuela duk kusan yadda ake shan fetur kaɗan ya ɗara a ce kyauta ake sha.

Daga Libya sai Iran da kuma Syria da Aljeriya da Kuwait. Waɗanda dukkansu galan 7 bai wuce Naira 750 ba. Angola da Nijeriya duk kusan Naira 1000 ake sayar da galan 1.

Sai dai kuma binciken ya nuna cewa a Hong Kong ake samun gas wanda ya fi na kowace ƙasa tsada a duniya. Daga Hong Kong kuma, sai ƙasar da ke take mata baya wajen tsadar gas, ita ce Netherland, daga nan sai Norway. Dala 13.10 ake sayar da lita 1 ta gas a Netherlands.

Daga cikin dalilan da ke haifar da tsadar su ne yawan sanya wa kamfanoni harajin da gwamnatoci ke ɗorawa.