NED—Makamin mallakar duniya

Spread the love

Daga AMINA XU

Asusun demokuraɗiyya na Amurka wato NED, ‘yan siyasar ƙasar sun yi masa laƙabin “ƙungiya mai zaman kanta dake baiwa sauran ƙasashe taimakon demokuraɗiyya”.

Amma a haƙiƙa dai fadar White Housa da ma majalisar dokokin ƙasar na samar masa kuɗi, kuma asusun yana bin umurnin gwamnatin ƙasar wajen jagorantar ƙungiyoyin masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa da su yayata manufofin Amurka da hambarar da mulkin ƙasashen ta hanyar samar musu kuɗaɗe.

Hakan ya sa ya kasance wani makami mai ƙarfi na Amurka don cin moriyarta da mallakar duniya.

Mai zana: Amina Xu

By Editor