BBC ta kitsa ƙarairayi kan batun ta’addanci

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Kwanaki sama da 20 da suka gabata, an kai farmakin ta’addanci kan wata mota ta kwalejin koyon harshen Sinanci, wato Confucius Institute dake jami’ar Karachi dake ƙasar Pakistan, al’amarin da ya haddasa mutuwar wasu malaman ƙasar Sin uku, tare da jikkata wani.

Kwamitin tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadai da irin wannan farmakin da kakkausar murya. Amma ita kafar yaɗa labaran BBC, ta wallafa wasu rahotanni kwanan nan, inda ta yi yunkurin wanke waɗanda suka kai farmakin daga mummunan laifin da suka aikata.

A matsayinta na ɗaya daga cikin kafafen yaɗa labaran ƙasashen yammacin duniya da suka taka rawa, abun da BBC ta yi, ba imani cikin sa ko kaɗan, wanda ya sa ta zama abokiyar gaba ga duk wani dake son shimfiɗa zaman lafiya a duniya.

Ko me ya sa wasu kafofin watsa labarai, kamar BBC, su kan nuna fuska biyu? Haƙiƙanin gaskiya ita ce, waɗannan kafofin yada labaran suna dogara kan manyan masu hannu da shuni na ƙasashen yamma, kana, a ƙasashen yamma, dukiyoyi da siyasa hade suke. A sabili da haka, ta hanyar fakewa da “neman ‘yancin yaɗa labarai”, wasu kafafen yada labaran ƙasashen yammacin duniya suna nasu aiki, domin bauta wa masu kuɗi da masu iko.

Yanzu ana iya fahimtar dalilin da ya sa wasu kafafen yada labaran yamma, suka yi yunƙurin ruwaito rahotanni, game da wasu jita-jitar da aka yada dangane da batutuwan da suka shafi Xinjiang da Hong Kong, sa’annan sun yi shiru, a yayin da wasu ke son bayyana gaskiyar abubuwan dake faruwa a Xinjiang da Hong Kong.

Fassarawa: Murtala Zhang

By Editor