Cikin shekara bakwai, APC ta yi ayyukan da suka gagari PDP

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta samu nasarori da dama fiye da kowace jam’iyya a Nijeriya a shekara bakwai da ta yi tana mulki.

Adamu ya bayyana haka ne a wajen taron ƙaddamar a kwamitin tantance ‘yan takarar majalisun jihohi a ranar Talata a Abuja.

Shugaban jam’iyyar ta bakin wakilcin mataimakinsa na shiyyar Arewa, Sanata Abubakar Kyari, ya jaddada cewa ba ya kokwanto daukacin ‘yan takarar da suka hadu a cibiyar tantancewa za su ci gaba da aiwatar da kyawawan manufofin jam’iyyar.

Da yake yi wa ‘yan kwamitin jawabi, Sanata Adamu ya ce, “Za mu iya bugun ƙirji da alfaharin cewa cikin shekaru bakwai da muka yi riƙe da ƙasa, mun samu nasarorin da wasu ba su iya samu ba. Don haka Shugaban Ƙasa zai bar kyawawan ayyukan da ya aiwatar ga magajinsa.”

Ya ci gaba da cewa, “Muna dab da zaben sabbin shugabannin da za su gaji mulkin Buhari, wannan ne ma ya sa aka zaɓe ku don cika wannan ƙuduri.

“Duba da irin mutanen da kwmaitin ya ƙunsa, ba na shakkar za mu yi abin da ya kamace mu. Siyasa aba ce mai canjawa haka ma buri. Za ku fuskanci ƙalubale da dama, amma kada ku bari ƙalubalan su dakusar da ku,” inji Adamu.

By Editor