’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 30 a hanyar Abuja-Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla fasinjoji 30 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Talata.

Wannan lamari dai ya zo ne sa’o’i 24 bayan gwamnatin tarayya ta sanar da buɗe hanyar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna wanda wasu gungun ‘yan bindiga suka daƙile shi, inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da mutane da dama a watan Maris ɗin 2022.

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar Kula da Jirgin Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta sanar da cewa, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayar da umarnin sake dawo da zirga-zirgar jiragen ƙasa a kan hanyar jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa hari, a ranar Litinin 23 ga Mayu, 2022.

A cewar NRC, gwamnati ta sanya ƙarin matakan tsaro a hanyar jirgin ƙasan da ke tashi daga Abuja zuwa Kaduna domin tabbatar da samar da isasshen tsaro ga fasinjojin da ke kan hanyar.

Sai dai ’yan bindiga sun mamaye babbar hanyar a ranar Talata, inda suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 30 a wani sabon hari da suka kai kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Rahotanni sun ce harin ya afku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Talata, inda da dama suka jikkata, ciki har da mata da ƙananan yara.

Wata majiya ta ce, “waɗanda abin ya rutsa da su na zaune a bakin hanya yayin da motoci ke ajiye a kan babbar hanyar.”

’Yan ta’addan sun kai wa fasinjojin Hukumar Sufuri ta Jihar Zamfara hari mai ɗauke da kujeru 18, Peugeot 406 ɗaya, Toyota Corolla biyu, mota ƙirar Golf, da wasu motoci da dama.

A cewar shaidun gani da ido, ’yan ta’addan sun bar wurin ne kafin isowar jami’an tsaro.

By Editor