Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
An dakatar da shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), reshen jihar Zamfara, Kanar Bala Mande (rtd) bisa zargin zagon ƙasa ga jam’iyyar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labarai na Jam’iyyar PDP na jihar, Abba Bello kuma aka miƙa wa Blueprint a Gusau ranar Laraba.
A cewar sanarwar, jam’iyyar ta ƙalubalanci shugaban jam’iyyar da aka dakatar, Kanar Bala Mande Rtd, kan gudanar da harkokin jam’iyyar ba tare da sa hannun kwamitin ayyuka na jiha ba, da kuma shugabannin jam’iyyar.
“Muna sanar da jama’a, da jiga-jigan ‘yan jam’iyyar mu mai girma ta PDP a Jihar Zamfara cewa an dakatar da shugaban jam’iyyar tamu, Kanar Bala Mande (rtd) saboda wasu ayyukan da suka saɓa wa jam’iyyar. .” Sanarwar ta karanta.
“Dakatar da shugaban jam’iyyar ya zama dole duba da yadda yake gudanar da harkokin jam’iyyar ba tare da sa hannun kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ba, da kuma shugaban jam’iyyar wanda hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu”.
“Jam’iyyar ta bayyana cewa matakin zai ba ta damar daƙile cin zarafi da kuma karkata ƙa’idojin tafiyar da jam’iyyar.”
Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, dakatarwar na tsawon wata guda ne domin bai wa kwamitin ayyuka na jam’iyyar na jiha kafa kwamitin bincike a kansa.
Jam’iyyar ta kuma umarci mataimakin shugaban shiyyar Ƙaura Namoda, Malam Ali Namoda da ya duba ayyukan jam’iyyar na tsawon lokacin da aka dakatar da shi.
Da yake mayar da martani kan dakatarwar da aka yi masa, Kanal Bala Mande (rtd) ya bayyana hakan a matsayin abin wasa, yana mai jaddada cewa har yanzu shi ne cikakken shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara.
