Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga hukumomin tsaron Nijeriya

Spread the love

Daga NAFI’U SALISU

Da Sunan Allah, Mai Rahama Mai Jinƙai.

Sanin kowa ne cewa, ƙarfin kowacce ƙasa da tsayuwarta a kan duga-duganta, ya ta’allaƙa ne bisa jajircewa da hoɓɓasa ta jami’an tsaronta, ta fuskar tsayuwa irin ta daga wajen tabbatar da tsaron ƙasa, kare rayukan al’umma da dukiyarsu. Wanda hakan shi ne abinda yake samar da ci gaban ƙasa musamman ta fuskar yaɗuwar arzikin ƙasa da bunƙasa ƙasa ta hanyar haɓaka tattalin arziki. Babu wata ƙasa da za ta cigaba, ta ɗaukaka matuƙar wannan ƙasa ta yi sake tare da riƙon sakainar kashi wajen al’amuran da ya shafi tsaro. Domin rashin inganta tsaro da ba shi kulawa ta musamman, wani babban al’amari ne mai matuƙar haɗari da muni, wanda ke iya haifar da rashin kwanciyar hankali ga ‘yan ƙasa. Kuma hakan yana hana wasu ƙasashe maƙwabta su shigo cikin duk wata ƙasar da babu tsaro domin kawo arziki, kamar cinikayya tsakanin ƙasa-da-ƙasa, ko saka hannun jari a cikin ita wannan ƙasar.

Al’amarin da yake faruwa a ƙasarmu Nijeriya, al’amari ne mai matuƙar ɗaure kai (amma ga talaka). Dalilin da ya sa nace ga talaka, saboda shi talaka kullum fafutukarsa ba ta wuce ya zai yi ya sami abinci ba, don haka bibiyar wasu al’amura da suka shafi ƙasa ba shi da wannan lokacin, domin an riga an jefa rayuwarsa cikin tsoro da fargabar rayuwa. Yadda lamarin tsaro ya lalace a Nijeriya, har ta kai ta kawo a yanzu babu wani mutumin Birni ko Karkara da yake da tabbacin idan ya fita daga gidansa zuwa kasuwa, gona, ko wani gari sada zumunci ga ‘yan uwansa, ko hulɗar kasuwanci da yake da tabbacin zai dawo gidansa lafiya.

Rayuwar da muke yi a yanzu, rayuwa ce mai cike da tsoro da fargaba. Dalili kuwa shi ne, idan ka fito zuwa kasuwa ba ka cikin kwanciyar hankali, haka idan ka tafi balaguro zuwa wani gari ba ka da tabbacin za ka isa wannan garin lafiya, haka ma idan kana dawowa gida. Idan ka shiga gidanka ka kwanta, shi ma kana cike da fargabar za a iya ɓalla ƙyauren gidanka a shigo, ayi kidnapping ɗinka a tafi da kai daga baya a nemi kuɗin fansa. 

To ina wani kwanciyar hankali ga ɗan Nijeriya, musamman wanda yake yankin Arewa? Don haka, tambayar da nake da ita a kan shugabannin rundunar tsaron ƙasarmu ita ce: shin ina alƙawarin da suka yi na cewar za su tsare rayuka da dukiyar al’umma? Ina kuɗaɗen da Gwamnatin tarayya take biyan su don tabbatar da haka? Shin ba su da makaman yaƙi da ɓata gari ne ‘yan ta’adda? Idan suna da makaman, to me ya sa ba sa yaƙar su?
Mun sani cewa Gwamnatin tarayya ƙarƙashin mulkin Muhammadu Buhari, ana biyan maƙudan kuɗaɗe ga rundunar tsaron ƙasar nan don tabbatar da tsaro, to amma me ya sa maimakon a samu galaba a kan ‘yan ta’adda sai kullum abubuwa suke ƙara lalacewa a fannin sha’anin samar da tsaro? Ko dai maganar nan da masu iya magana suke cewa, “Rijiya ta ba da ruwa guga ta hana” ne yake faruwa a wannan qasa? Idan haka ne, to menene ribar jami’an tsaro a kan rashin yi da gaske don magance matsalar tsaro?

Daga lokacin da mai girma shugaban ƙasar Nijeriya,  Muhammadu Buhari ya zamo shugaban ƙasa zuwa yau, bincike ya tabbatar da cewa an samu ɓatan makamai a hannun rundunar tsaron Nijeriya. Bayan kafin haka, duk wani kasafi da shugaban ƙasa zai yi sai an ware maƙudan kuɗaɗe a fannin sha’anin tsaro don tabbatar da tsaron, to amma har yanzu abin ya gagari kundila. Haka nan mun ga irin makamai da motoci gami da jiragen yaƙin da ake sayowa don yaƙar ‘yan ta’adda a ƙasar nan, amma shi ma abin ya zamo tamkar wasan kwaikwayo.

Abin haushi da takaici abin da ya faru kwanannan a jihar Kaduna, kan hanyar Kaduna zuwa ƙaramar hukumar Birnin Gwari (tsakanin wani gari Falwaya da Oduwa) inda Gwamnati ta ajiye sojoji don daƙile harin ‘yan ta’adda, amma sai aka wayi gari su ‘yan ta’addar sun yi wa jami’an sojojin dirar mikiya rana tsaka suka buɗe musu wuta, al’amarin da mazauna yankin suka kira shi da mummunan harin da ba su taɓa ganin irinsa ba. Domin kusan duk wanda za ka ji wannan labarin daga bakinsa wanda shaidar gani da ido ne, zai faɗa maka cewa ‘yan ta’addar sun kai kimanin mutum dubu ɗaya. A wannan harin an kashe sojojinmu da basu ji ba, ba su gani ba. Sannan an ƙona musu motocin yaƙi guda uku. Shin a haka za mu yi ta gani muna jin munanan hare-haren ta’addanci irin wannan? Waɗannan fa jami’an tsaro ne, kuma jami’an tsaron ma sojoji ba ‘yansanda ba, shin ina ga kuma mutanen ƙauye waɗanda za ka samu wasu ba su da ko wuƙar yanka kaza a gidansu sai sun aro daga maƙwabta?

Tsakani da Allah manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan ku ji tsoron Allah, ga dukkan alamu wannan al’amarin na rashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki a kan ‘yan ta’adda don kawo ƙarshen matsalar tsaro, abu ne da ba ku ɗauke shi da muhimmanci ba. Shi ne zai bamu tabbacin cewa ba da gaske kuke yi ba don murƙushe ta’addanci da ‘yan ta’adda ba. Idan su ƙananun sojoji da ake tura su yaƙar ‘yan ta’adda da gaske suke aikinsu, to ku na sama da su ba da gaske ku ke yi ba. Shi ya sa wasu suke yi muku kallon kun maida wannan al’amari na rashin tsaro kasuwanci. Kuna kasuwanci da shi, kuna tara haramtaccen kuɗi don kawai more rayuwarku ta nan gidan Duniya. Amma wallahi tallahi ba da gaske kuke yi ba, domin da a ce da gaske kuna son kakkaɓe matsalar rashin tsaro, to zuwa yanzu ba za a samu sauran wani ɗan ta’adda a cikin ƙasar nan ba, tuni kun kakkaɓe shi.

Sannan akwai wani babban al’amari wanda shi kansa ƙalubale ne ga tsaron ƙasar nan, wannan abu kuma sananne ne a bayyane yake a fili ba a voye ba. Ina magana ne a kan yadda jami’an tsaro suke karɓar kuɗaɗe a hanya a hannun matafiya da direbobin motoci, wanda shi ma kansa wannan babban abin dubawa ne. A da idan ka ɗauki kuɗi ka ba jami’in soja a matsayin cin hanci, to sai ka cinye wannan kuɗin, sannan kuma za ka sha gwale-gwale. To amma yanzu abin ba haka yake ba, su kansu jami’an soja sun gane daɗin karɓar kuɗi wajen direbobi a shingen jami’an tsaro, wanda wannan hatsari ne babba ga tsaron qasa. Idan har jami’in tsaro zai tsaya a kan hanya, direba ya taho da fasinja a motarsa ya ɗauki kuɗi ya baiwa jami’in tsaro, shi kuma jami’in ya karva ya bar shi ya wuce, to wannan abu ne mai sauƙi shi direban ya ɗauko kayan laifi a motarsa, ko kuma ya ɗauko fasinja mai kayan laifi su zo su wuce ba tare da an gane komai ba saboda Naira ɗari ko hamsin ce za ta ba shi damar wucewa da kayan laifin.

An sha kama irin waɗannan a wasu wuraren, to sai dai ko an kama, ba a yin hukuncin da ya dace. Shi ya sa al’amarin yake qara ƙazanta. Yanzu akwai shingen binciken da idan ka zo wajen za ka ga an rubuta a jikin symbol cewar  ‘karvar cin hanci a nan laifi ne’ to amma da direba ya tsaya za ka ga ya ɗauko kuɗin ya miqa jami’in tsaro ya karɓa, shikenan sai ku wuce. Wannan fa babban ƙalubale ne wanda yana ɗaya daga cikin manya-manyan abubuwan da suka jawo lalacewar tsaro a ƙasar nan, kuma na tabbatar Gwamnati tana sane da wannan, haka su ma manyan hafsoshin rundunar tsaro za su san wannan. To amma me ya sa ake cigaba da yin wannan babu wani mataki da ake ɗauka?

Duk wata hanya da aka girke jami’an tsaro a kudu da Arewacin ƙasar nan, babu wani shingen bincike da jami’an tsaro basa karvar kuɗi a hannun direbobi. Hakanan kuma sanin kowa ne su jami’an tsaron haƙƙinsu ne su tsare rayuka da dukiyar al’umma bisa tsarin dokar ƙasa. Baya ga haka kowanne ma’aikaci yana da alawus na kuɗin abinci a kowacce rana, sai kuma albashinsa da yake karɓar a wata-wata. Idan haka ne, to menene dalilinsa na karvar kuɗi wajen farar hula? Idan ya ce yana tsaye a cikin rana, ko cikin daji yana tsare al’umma? Shin al’umma ne suke da alhakin su biya shi wannan aikin da yake yi ko kuwa Gwamnati? Kenan kuɗin da jami’in tsaro zai karɓa a hannun direba ko matafiyi, to menene matsayin karɓar wannan kuɗin, tunda gashi yana karɓar kuɗin amma ba a fasa tare fasinja a hanya a yi garkuwa da su ko a kashe su ba.

Maganar gaskiya a nan ita ce, ya zama dole Gwamnati ta binciki manyan jami’an tsaro a kan rashin samar da tsaro, sannan kuma dole ne hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam su tsaya su yi aikinsu tsakani da Allah, matuƙar suna amsa sunansu na hukumar dake kare haƙƙin ɗan Adam. A hanyar ƙaramar hukumar Birnin Gwarin jihar Kaduna, jami’an tsaro suna karɓar kuɗi a hannun kowanne direba (N1,000) suna yi musu rakiya don fitar dasu cikin dajin da ake tare mutane ayi garkuwa da su ko a kashe, wanda kuma a ƙalla duk rakiya ɗaya a kan tara mota ashirin zuwa talatin. Idan an kai waɗannan a can inda aka raka su za a sami wasu suna jiran idan an kawo wasu suma a koma da su, su ma kuma dubu-dubu za su biya. Kullum a haka ake a hanyar Kaduna zuwa ƙaramar hukumar Birnin Gwari, duk wanda yake bin wannan hanyar ya san ana yin wannan. To yanzu don Allah kuɗaɗen da wadannan jami’an tsaron suke tarawa a kullum kuna ganin cewa za su so wannan hanyar ta yi lafiya? To kun ga kenan laifin jami’an tsaro ne, domin kasuwanci suke yi a hanyar ba su da fatan al’amarin kashe-kashe da garkuwa da mutane ya qare a wannan hanya.

Sannan abin takaici, wallahi tallahi duk wani direban babbar motar da yake son ya bi hanyar Funtua daga Birnin Gwari ya zo Ɗandume ko Funtua, ko Bakori ya shigo Malumfashi ko ya tafi Katsina, matuƙar ya zo wajen barikin sojojin sama dake kan hanyar Funtua a cikin garin Birnin Gwari, to waɗannan jami’an tsaron suna hana manyan motoci wucewa sai su ce su koma su bi ta hanyar Kaduna, dalili saboda suna karɓar dubu-dubu a hannunsu. Hanyar zuwa Funtua kuwa daga Birnin Gwarin lafiya ƙalau direba zai biyo ta ya wuce babu wanda zai ce masa ƙala a yanzu haka, amma a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna kuwa dole sai an yi maka rakiya, kuma dole sai ka biya kuɗin rakiya dubu ɗaya. Sannan duk da wannan rakiyar da jami’an tsaron suke yi, hakan ba ya hana a tare a yi garkuwa da mutane ko a kashe ba. 

To ya kamata manyan jami’an tsaron ƙasar nan ku tsaya ku yi aiki bil-haƙƙi da gaskiya, idan ba ku san meke faruwa ba a yankunan da ake fama da rashin tsaro ya kamata ku tashi tsaye ku bincika kuma ku sani. Ba ma zai yiwu a ce ba ku sani ba, tunda akwai jami’an farin kaya da suke shiga ko’ina, kuma suna zuwa da rahoton abinda suka gani. Sannan ku sani cewa, idan har wannan ta’addancin da ake aikatawa a yanzu ba a magance shi ba, wallahi tallahi har ku ba za ku tsira ba. Don haka ya zama dole ku ji tsoron Allah, ku cire son zuciya, ku daina kwaɗayin tara abin duniya, domin duk abinda mutum ya samu na dukiya ko wani kayan alatu na jin daɗin rayuwa, to a nan duniya zai tafi ya bar shi. Kuma akwai hisabi a gaban Allah ranar Alƙiyama. Sannan duk wanda ya haɗa kai da ɗan ta’adda don a lalata ƙasa da rashin tsaro, shi kuma a gefe yana tara kuɗi, to wallahi ya kwana da sanin cewa gawar Fir’auna tana nan a ajiye Allah Ya bar ta a bayan ƙasa don ta zamo izina ga duk wani azzalumi.

Babu wani jami’in tsaron da zai tsaya ya sadaukar da rayuwarsa don kare haƙƙin ‘yan qasa face sai Allah ya ba shi kariya, duk kuma wanda ya haɗa kai da ɓata-gari ake kashe al’umma, wallahi tallahi ba zai taɓa yin rayuwa a cikin farin ciki ba, kuma zai yi mutuwar wulaƙanci. Don haka ku ji kuma ku sani, jarumta ita ce jajircewa wajen yin aiki don Allah da kare rayuka da dukiyar al’umma, ba ƙarin girma ko tara dukiya da gina gidaje ko hawa manyan motoci ba. Tabbas a cikin ƙananun jami’in tsaro akwai waɗanda suke da zuciyar tsayawa a mutu ko a yi rai don yaƙar ‘yan ta’adda, amma hakan ba zai yiwu ba har sai ku manyan jami’an tsaro da kuke ba da umarnin a yi, ko a bari kun ƙarfafa musu gwiwa wajen tabbatar da adalci da kuma saka kishin ƙasa da al’ummar ƙasa a zukatanku.

Nafi’u Salisu
(Marubuci/Manazarci)
[email protected]
[email protected]
08038981211

By Editor