Numfashin mutum (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

‘Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkanmu mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan Adam, domin ku fa’idantu, ku san yadda jikin ku ke aiki.

Satin da ya wuce, na fara bayanin yadda jini taimakawa wajen musayar iska tsakanin duniyar da muke ciki, da kuma duniyar jikin ɗan adam. Mun tsaya a inda nake cewa:

Huhun mutum na dama da na hagu, sun sanya zuciya a tsakiya. Saboda hikima da fikra ta Sarkin halitta, hakan na da wani sirri da zai tabbatar da kasancewar mutum a raye. Zuciya tana harba jini mai ɗauke da iskar CO2 , ciki huhu, inda a nan ne za a cire ita iskar CO2 din daga cikin jinin sannan a zuba iskar oksisjin. Jinin yana bi ne ta ta hanyoyin jinin da suka tashi kai tsaye daga zuciya zuwa cikin huhu, ana kiran su da “pulmonary arteries”. Bayan an sanya wa jinin iskar O2, jinin zai biyo ta wasu hanyoyin jinin daga huhu, ya dawo zuciya, ana ace musu “pulmonary eins.”

Shigar waɗannan hanyoyin jini cikin huhu ke da wuya, sai su dinga biyewa rassan bututun iska, har izuwa inda rassan bututun iska suke ƙarewa a matasayin ‘buhun musayar iska’. A cikin huhun mutum, akwai buhhunan musayar iska masu yawan gaske, wanda sun kai kimanin miliyan 200 zuwa miliyan 300 a yawa. Kowanne kewaye yake da hanyoyin jini da suke taka rawa wajen musayar iska. Wadannan ‘yan ƙananan hanyoyin jini ana cewa dasu: “pulmonary capillaries.” Musayar iska na faruwa ne a wannan mataki: wato tsakanin hanyoyin jinin da kuma buhun musayar iska, kamar yadda za mu gani nan gaba kadan.

Huhun mutum, na dama da na hagu kewaye suke da tantani ruɓi biyu, waɗanda ake kira da ‘pleurae’. Ruɓin farko, wanda yake daga ciki, a manne yake da jikin huhu; kuma kamar farar leda yake. Shi ke sanya huhun ya dinga ƙyalli, kamar an shafe shi da mai. Shi kuma rubi na biyu na waje, kewaye yake da huhun, amma bai manne da jikin huhun ba. Saboda haka a tsakanin wadannan rubi guda  biyu, akwai wata ‘yar karamar rata ko ince ‘space’ a turance, wanda yake dauke da wani tsinkakken ruwa mai santsi.

Amfanin wannan ruwan shi ne sauƙaƙe kaushin gugar da ke faruwa tsakanin ruɓi biyun rigar tantanin da ta rufe shi, da kuma kiyaye shi daga siɗewa saboda gugar da ke faruwa wato “friction” tsakanin huhu da sauran halittun dake makwabtaka da shi, tun da ko da yaushe, huhu a cikin motsi yake.

Ɗaya daga cikin abubuwan ban mamaki a jikin dan adam, shi ne banbancin da ake samu tsakanin tagwayen halittu. Misalin tagwayen halittu sun hadar da: ƙoda, idanu, kunnuwa, hannaye da sauran su. A wannan gabar, ya dace kusan cewa huhun dama da na hagu suna da banbanci. Huhun dama, ya dan fi huhun hagu girma. Sannan huhun hagu ya dan fi na dama tsawo. Haka kuma, huhun dama yana da tsaga: ‘fissures’ guda biyu, da suka kasa huhun gida 3 wato tsagin sama, na tsakiya, dana qasa; shi kuma huhun hagu, yana da tsaga ɗaya a kwance, da ta raba shi zuwa gida biyu: tsagin sama da na kasa. A cikin kowanne tsagi, akwai rassan bututun iska da hanyoyin jinin da ke mara musu baya.
Kowanne huhu, yana da shatin halittun da suka bi ta jikin sa. Babban misali shi ne bututun abinci  ya bi ta tsakanin huhun hagu da na dama, saboda haka ya bar shati a jikin kowanne huhu. Daga nan kuwa shi bututun abincin ya wuce izuwa kogon ciki, wato ‘abdominal cavity’. Wani misalin shi ne huhun hagu yana da shatin alamar inda goshin zuciya yake, daga qasa. Kasancewar goshin zuciya ya kutsa jikin huhun hagu, shi yasa mafi yawan mutane ke tunanin zuciyar mutum daga bangaren hagu take.

Ina ga bari in bar magana game siffa ta zahiri ta huhun mutum, kar mu yi nisa ya zamto mai karatu ya dena hango ko da ƙura ta. Yanzu zan ɗauki wata gaɓar da take taka muhimmiyar rawa yayin da muke numfashi.

Kogon ƙirji, an gina shi ne daga kasusuwan haƙarƙari, da tsokar naman dake tsakanin kowanne kashin hakarkari.  Daga gaba, kasusuwan hakarkari suna da guntsi da ya ke haɗuwa da ƙashin tsakiyar kirji, wato ‘sternum’. Daga baya kuwa, kasusuwan haƙarƙari suna haɗewa ne da ƙashin baya wato ‘backbone’.

Shi kogon ƙirji, an gina shi ne da kashin hakarkari, wanda ake samun tsokar nama a tsakaninsa. Yana bada kariya ga huhu, zuciya, da halittun da ke maƙwabtaka da su. Kamar yadda huhu yake budewa yayin da iska ta shiga cikin sa, sannan ya tsuke yayin da iska ta fita daga ciki, haka shi ma qashin haƙarƙari ke yi. Idan iska ta shiga cikin huhu, kogon haƙarƙari sai ya buɗe domin ya bawa huhu damar buɗewa, saboda iska ta shigo cikinsa. Hakazalika idan iska zata fita, kogon haƙarƙari sai ya tsuke, shima huhu haka.

Akwai kuma shamakin tsoka da ya raba tsakanin kogon ƙirji (a sama) da kogon ciki (a ƙasa) wanda a turance ake kira da “diaphragm.” yana taka muhimmiyar rawa wajen shigar iska cikin huhu. Yayin da mutum ya shaki iska, wannan tantani zai yi ƙasa ne saboda ya kara girman kogon ƙirji, saboda huhu ya samu damar walawa. Idan kuma mutum ya fitar da iska waje, sai tantanin yayi sama, domin ya rage girma da faɗin kogon ƙirji.

Numfashi yana ƙarƙashin kulawar cibiyoyin kula da numfashi wadanda suke da tasha a ƙwaƙwalwa da kuma laka. Waɗannan cibiyoyi suna da muhimmanci ƙwarai, domin su ne ke aiki a lokuta daban daban yayin da kake numfashi. Kuma suna saisaita yanayi na numfashi. Idan yayi kasa, za su gyara, haka ma idan numfashi yayi sama, za su gyara.

Shin an taɓa fusata miki rai? Na san an taɓa, ko da kuwa sau ɗaya ne. Ya kika ji numfashinki a wannan lokaci? Shin Ka taɓa shiga wani yanayi na firgici a ƙanƙanin lokaci? Na san ka taɓa, ko da kuwa sau ɗaya ne. Ya ka ji numfashinka a wannan lokacin? A duk misalan nan guda biyu da na kawo, cibiyoyin numfashi a ‘tsaye’ suke, domin kula da duk wani sauyi, da tabbatar da tafiyar komai yadda ya kamata.

A lokutan da kuke cikin kwanciyar hankali, da kuma halin bacci, waɗannan cibiyoyi na tabbatar da cewa mutum yana numfashi a hankali. Amma yayin da aka samu sauyi, misali mutum ya yi motsa jiki, ko ya shiga waje mai hayaƙi, ko yanayi na razana ko firgita ko fusata, hakan zai ingiza bugun zuciya, da kuma sanya fitar numfashi da sauri, waɗannan cibiyoyi zasu yi ta aiki har sai numfashi ya dawo yadda ya kamata, wato sau 18 zuwa sau 20 a duk minti guda.

Yadda wadannan cibiyoyi ke gudanar da aikin su shi ne ta hanyar sadarwa ta cikin ‘wayarin na jikin mutum’, ko kuma ‘jijiyoyin motsi’. Da akwai jijiyoyin motsi da suka tashi daga jikin tantanin da ya raba kogon ciki da kogon ƙirji, wato “diaphragm” izuwa cibiyar numfashi. Kun ga nace yana yin ƙasa yayin da mutum ya sheƙi iska, sannan yayi sama yayin da mutum ya fitar da iska. To tun da kuma yana da wayarin da ya dangane izuwa cibiyar kula da numfashi, ashe kulawa da daidaita numfashi ba zai wahala ba.

Haka kuma akwai jijiyoyin motsi da suke jikin huhu, da rigar huhu wato “pleurae”, da kuma tsokokin da ke tsakanin kafofin da ake samu a kasusuwan hakarkari. Waɗannan jijiyon motsi su ma suna kula da daidaita numfashi.

Ka tava zama kayi tunani akan iskar da kake shaka kullum? Shin ko kasan dame dame ye a cikin ta, kuma meye tasirin abubuwan dake cikin ta game da lafiyar Ka? Iskar nan da kuke gani, haɗe-haɗen sinadarai ne suka tada ita.

A cikin bayanai na, za ku fuskanci na yi magana akan iskar oksijin, da iskar kabon dai ogzayid. Haka nan akwai iskar nayiturojin, wadda idan babu ita acikin iska, komai da kake gani sai ya kone! Ita iskar nayiturojin tana sirka karfin tasirin iskar dake duniyar mu ne, don kada abubuwa su dinga kama wa da wuta.

Akwai danshi a cikin iska, akwai kuma sindarai waɗanda kan tallafawa rayuwar ka, da kuma waɗanda kan iya illata ta, duk a cikin iska. Anyi kiyasin cewa ‘yan ƙananan sinadarai dake cikin iska suna da matukar yawa da har sun ɗara tiriliyan biyu! Kuma cikin ƙudura ta Rabbul Izzati, sai ya gina jikin ku da naawa, yadda a ɗabi’ance, iskar oksijin kaɗai zamu shaka, sannan mu fitar da maras kyau, wato iskar kabon dai ogzayid.

Mu haɗu sati mai zuwa idan Sarkin ya kai mu, domin kawo muku bayanin yadda numfashi ke kasancewa, da rawar da wadannan iskoki kala biyu ke takawa domin kasancewar mu a raye.