
Daga BELLO A. BABAJI
Wani ɗalibi da ke rubuta jarrabawar WAEC mai suna Taiwo, ya rasa ransa a lokacin da ƴan sanda suka yi harbi yayin wani atisaye a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo.
Lamarin ya auku ne a kusa da kasuwar Gbagi dake yankin Soka a birnin, ranar Litinin.
Wani shaida ya ce, jami’an ƴan sandan suna farautar ƴan damfara ta yanar gizo ne da aka fi sani da ƴan yahoo a lokacin da abin ya faru, inda ɗaya daga cikinsu ya yi harbin da ya samu ďalibin, wanda ke cikin motar mahaifinsa a hanyarsa ta zuwa rubuta jarrabawa.
Lamarin da ya fusata al’umma a yankin inda suka yi cincirindo a titunan birnin tare da ɗaukar gawar mamacin zuwa sakatariyar gwamnatin jihar dake Agodi.
Sun buƙaci a yi musu adalci tare da gaggauta binciken gano wanda ke da hannu a aikata laifin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Adewale Osifeso ya tabbatar da cewa tuni aka fara gudanar da bincike akan al’amarin tare da alkawarin ɗaukar matakin doka a kai.
