William Shakespeare: Marubucin da bai taɓa mutuwa ba a Adabin Ingilishi

Spread the love

Zan fi zaɓar in kasance da gaskiya fiye da in birge mutane – Shakespeare

“Komai yana da lokacinsa, kuma duk abin da ke faruwa yana faruwa bisa dalili”

Daga AISHA ASAS 

A cikin tarihin adabin duniya, babu wani suna da ya fi girma da ƙayatarwa fiye da William Shakespeare. An san shi da ƙwarewa mai zurfi a fagen rubuce-rubuce, wasan kwaikwayo, da waƙa, inda ya haifar da wani gagarumin sauyi a harshen Ingilishi da kuma yadda ake fahimtar ɗabi’ar ɗan adam. Shakespeare ba kawai marubuci ba ne, domin ya kasance wani ginshiƙi ne da ya sauya fasalin adabi gabaɗaya. Rubuce-rubucensa sun ci gaba da rayuwa fiye da shekaru ɗari huɗu, kuma kalmominsa sun ratsa al’adu, harsuna da zamani. Wannan ne dalilin da ya sa ya rayu har zuwa wannan lokacin. 

Kafin mu yi nisa ga bayyana namijin ƙoƙarin da marubucin ya yi wa adabin Ingilishi, bari mu fara da tambayar shin wane ne William Shakespeare?

Shi dai Shakespeare an haife shi a garin Stratford-upon-Aɓon a shekarar 1564. Mahaifinsa John Shakespeare ɗan kasuwa ne, yayin da mahaifiyarsa Mary Arden ta fito daga dangin manoma masu daraja. Shakespeare ya taso cikin ‘yan uwa har guda takwas, kuma ko da yake ba a tabbatar da cewa ya je jami’a ba, zurfin fahimtarsa da natsuwarsa a rubuce-rubuce sun fi bayyanar da ilimi fiye da takarda.

Yana da shekara 18 ya auri Anne Hathaway,wadda ta girme shi da shekaru takwas, kuma sun haifi ’ya’ya uku, Susanna, da kuma Hamnet da Judith,  waɗanda suka kasance tagwaye. Kamar yadda tarihi ya nuna, Shakespeare ya fara haɗuwa da tangarɗa a sha’anin rubutu, bayan da ya rasa ɗansa Hamnet a lokacin da yaron yake da shekaru 11 da haihuwa. Baƙin cikin wannan rashin ya kawo tazgaro ga harkar rubutunsa a lokacin. 

A shekarar 1590, Shakespeare ya bar garinsu ya koma London, inda ya tsunduma cikin harkar wasan kwaikwayo. A can ne ya yi fice cikin ƙungiyar ‘The Lord Chamberlain’s Men’, wadda daga baya ta zama ‘The King’s Men’. Ya rubuta wasannin kwaikwayo kusan 39, waƙoƙin sonnet 154, da waƙoƙi masu tsayi guda biyu.

Wasanninsa sun kasu kashi uku: 

Na baƙin ciki (tragedies)

Na barkwanci (comedies)

Na tarihi (histories). 

Ayyukan rubutun da ya yi kamar ‘Hamlet’, Othello, Macbeth, da ‘King Lear’ suna nuna yadda yake zana ruɗanin ɗan adam cikin salo da falsafa. A cikin waɗannan wasanni, Shakespeare yana bayyanar da rikice-rikicen zuciya, halaye, kishirwar iko da tasirin laifi. Rubuce-rubucensa suna cike da hikima da maganganu masu ƙarfi waɗanda suka zama karin magana a duniya.

Wasu daga cikin kalmomin sa da suka shahara sun haɗa da:

“All that glitters is not gold.” (Ba komai mai sheƙi ne zinari ba.)

“To thine own self be true.” (Ka kasance da gaskiya ga kanka.)

“Cowards die many times before their deaths.” (Jin tsoro yana kashe mutum fiye da sau ɗaya.)

Baya ga fasahar canje-canjen halaye, Shakespeare ya taka muhimmiyar rawa a fagen ilimi, siyasa da falsafa. Wasanninsa na tarihi kamar ‘Julius Caesar’ da ‘Coriolanus’ suna bayyana rawar da iko ke takawa a zamantakewar ɗan adam, yayin da labarinsa ‘The Tempest’ ke zayyana batun adalci da tubabbun shugabanni. Malamai a duniya sun yi amfani da ayyukansa wajen koyar da darussa kan shugabanci, nazari da halaye. Ayyukan sa sun ba da gudunmawa wajen fahimtar mahimmancin harshe, ikon kalma, da tasirin ruhi a zuciyar ɗan adam.

Masana kamar Sigmund Freud da Friedrich Nietzsche sun nazarci halayen jarumansa don gina ra’ayoyinsu. Haka kuma, Shakespeare ya taimaka wajen faɗaɗa harshen Turanci da ƙirƙirar sababbin kalmomi fiye da 1,700. Fina-finai irin su ‘The Lion King’ (daga Hamlet) da West Side Story (daga ‘Romeo and Juliet’) sun samo asali daga zancen sa. Waƙoƙin sa sun haifar da darussa a duk faɗin duniya.

A yau, akwai darussa na musamman a jami’o’i da dama na duniya, inda ɗalibai ke nazari kan Shakespeare daga fannoni da dama: harshe, siyasa, zamantakewa, al’ada da tunani. Ayyukansa ana ci gaba da fassara su zuwa harsuna sama da ɗari, kuma ana girmama rayuwarsa da gudunmawarsa ta hanyar bukukuwan shekara-shekara a Ingila da Amurka da ma sauran duniya.

Shakespeare ba kawai marubuci ba ne, ya kasance wani gini ne da duniya ta ɗora adabinta a kai. Kamar dutse ne da aka kafa gaɓar fahimtar ɗabi’ar ɗan adam a kansa. Ko da yake ya rayu a zamanin da fasahar zamani bata kai matsayin yau ba, maganarsa ta rinjayi kowane ƙarni da kalma guda. Idan aka ce Shakespeare yana da ikon haye zamani, hakan gaskiya ce, saboda yadda ya fahimci zuciyar ɗan adam har fiye da masana kimiyya da falsafa.

Fasaharsa ba ta tsaya ga ba da nishaɗi ba kawai, har da shiga cikin zuciyar tunani: shin menene gaskiya? Menene iko? Ta yaya kishin ƙasa ko soyayya ke iya lalata mutum? A cikin Hamlet, sai ka ga ruɗanin mutum da tambayoyin da ba su da sauƙin amsa: “To be or not to be?” Wannan ba tambaya bace kawai, ishara ce daga cikin kiran da Shakespeare ke yi ga kowanne mutum ya tsaya ya sake duba rayuwa.

Wani babban abu da ya bambanta Shakespeare da sauran marubuta shi ne, yadda yake sanya ƙaramin abu ya zama madubi ga duniya. Wasu lokuta soyayyar ’yan biyu a wani wuri kamar ɓerona tana zama hanyar magana kan rikicin zamantakewa. Wasu lokuta ruɗanin wani sarki ya wakilci rudanin kowanne mutum da ke neman adalci ko gafara. Shi ya sa ko da jaruman sa na wasu ƙasashe ne Italiya ko Ingila duk abin da suke faɗa da aikatawa yana magana da zuciyar kowa, a koina.

Har ila yau, Shakespeare ya kasance wani gagarumin jigo wajen tallafa wa harshen Turanci. Kalmoninsa da ya ƙirƙira sun cika yawun masu magana da harshen ba tare da sun sani ba. Wasu daga cikin maganganunsa sun zama tushen rayuwar yau da kullum, kamar su: “The world is your oyster” (Duniya tana hannunka), ko “Wear your heart on your sleeɓe” (Bayyana abin da ke zuciyarka a fili). Wannan yana nuna cewa Shakespeare ba wai kawai ya kasance marubuci ba ne, face mawallafin wata hanyar magana da nazarin mutane.

A fagen addini da ɗabi’a, Shakespeare ba ya wa’azi kai tsaye, amma ayyukansa sun cika da ƙyallin hikima. A cikin Measure for Measure, ya ɗaga batun adalci da gafara cikin salo da ke cusa tambaya: shin ya dace a hukunta mutum bisa dokar da ba shi kaɗai ke karya ta ba? A cikin ‘The Merchant of ɓenice’, ya nuna yadda ɗan adam ke yanke hukunci bisa launin fata, addini da ra’ayi. Wannan batutuwa ne da har yanzu duniya ke fama da su.

Ya kamata a lura da yadda Shakespeare ya nuna mata cikin salo da girmamawa, wanda ya sha bamban da yawancin marubutan zamaninsa. Jarumai irin su Portia (a The Merchant of ɓenice), ɓiola (a Twelfth Night), da Lady Macbeth sun sha bamban da taswirar mata da aka saba gani a lokacin. Portia ta fi mazan da ke kusa da ita wayo da hangen nesa. ɓiola ta nuna ƙarfin hali da hikima duk da kasancewar ta mace. Lady Macbeth kuwa, duk da mugunta, tana bayyana ƙarfin zuciyar mace da yadda za ta iya rinjayar duniya.

A yau, Shakespeare ya fi zama a cikin zuciya da ruhi fiye da abin da zai iya zama a kabari. Daga canje-canje na zamani zuwa fina-finai, daga waƙoƙin hip hop zuwa waƙoƙin gargajiya, zuwa dandalin Twitter, suna ayyukansu ne bisa tubalin da ya gina. Idan akwai wata murya da ke ratsa ƙarnuka da harsuna, to tabbas ta Shakespeare. Kalmominsa sun yi tasiri matuƙa a zukata da ayyukan mutane, sun yi zurfi tamkar raƙuman teku.

Don haka idan muka ce Shakespeare ya rayu har yau, ba mu yi kuskure ba. Bai mutu ba. Bai gushe ba. Ya rayu ne cikin nunfashin adabi, cikin harshen zuciya, cikin maganganun rayuwa. Kuma kowanne karatu na bayyana sashen rubutunsa.

Duk da shahararsa, akwai wasu abubuwa cikin rayuwar Shakespeare da har yanzu ke cike da duhu da al’ajabi, tare da saka ayar tambaya. Misali, tsakanin shekarar 1585 da 1592 lokacin da ya bar garinsu bayan haihuwar tagwayensa, ba a san inda ya je ba, kuma masana sun kira wannan lokaci da “shekarun ɓacewar sa” (The Lost Years). Wasu na ɗauka cewa ya je koyarwa ne a wata makaranta, wasu kuma suna tunanin ya shiga cikin harkokin kasuwanci ko tafiya don neman ilimi. Wannan ɓangaren rayuwarsa har yau ba a samu wani ƙarin bayani kansa ba.

A fagen siyasa kuma, duk da cewa Shakespeare bai yi rubuce-rubuce kai tsaye akan lamuran siyasar zamaninsa ba, akwai alamun cewa yana da fahimta mai zurfi game da yadda iko ke tafiya da yadda zai iya lalata rayuwar ɗan adam. A cikin Macbeth, muna ganin yadda kwaɗayin iko ya rusa mutunci da tausayi. Wannan ya nuna cewa Shakespeare yana kallon siyasa ba kawai a matsayin mulki ba, har da a matsayin wani gwajin ɗabi’a da kuma jarabtar zuciya.

Abin mamaki shi ne, yadda Shakespeare ya fi bayyana addini cikin ɗaukar matsakaicin ra’ayi ba tare da nuna bambancin aƙida ko tsattsauran ra’ayi ba. Wannan yana da amfani musamman a lokacin da ya rayu, lokacin da Ingila ke fama da rikice-rikicen addini sakamakon Katolika da Anglicanism. Yana kaucewa kushe ko goyon bayan wani ɓangare kai tsaye, sai dai ya bar tambayoyi a cikin jarumansa su bayar da falsafar da ke cikin zuciya.

Bugu da ƙari, akwai ra’ayoyi da dama masu ƙarfi da ke nuna cewa, Shakespeare ya kasance mai fahimta game da ɗan adam, irin su ilimin halitta, matsalolin hauka, da tsoron mutuwa, waɗanda har yanzu masana ke amfani da su a matsayin hanyar nazari. Hamlet ya bayyana mutum da ke fama da bacin rai da kuma ruɗani; King Lear yana fuskantar hauka da karyewar zuciya. Wannan fahimta mai zurfi ta sa Shakespeare ya zama kamar wani likitan halayyar ɗan adam, wanda ke nazarin zukata da laifin da take ɓoyewa.

A cikin lokacin ƙarshen rayuwarsa, Shakespeare ya koma Stratford-upon-Aɓon, inda ya kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da ya ba shi damar morar dukiyarsa. Duk da ya janye daga sha’anin rubutu a wannan lokacin, hakan bai sa haskensa dishewa ba. Har yau, ana ci gaba da bincike a kansa, ana ƙirƙirar sabbin fassara da gwaje-gwaje bisa ayyukansa. Dukkan wannan yana nuni da cewa Shakespeare ya ƙetare iyaka, lokaci, da al’ada, ya koma wata irin murya ce ta ɗan adam da ke cikin kowanne zamani.

William Shakespeare ya rasu ne a ranar 23 ga watan Afrilu, shekara ta 1616. Saidai za mu iya faɗa da babbar murya cewa, har yau bai mutu a zukatan mutane ba. Ya rayu tsayin waɗannan shekarun ne ta sanadiyyar rubuce-rubucen da ya yi, waɗanda suke ɗauke da dogon nazari da hangen nesan da ya kawo shi har a wannan ƙarnin.

Da haka zan iya cewa, yawan littafai ba shi da alaƙa da tasirin marubuci ko jimawar sa a rayuwar makaranta, a maimakon haka, littafi ɗaya tal zai iya rayar da marubuci har a lokacin da jikokinsa suka gushe.

By ukarofi