Ta’addanci: ’Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane biyar a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutun biyar sun mutu,wasu biyar sun sami raunuka daban-daban sakamakon hare haren ‘yan bindiga a ƙauyen Gobirawa a ƙaramar hukumar Dutsinma.

Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ‘yan bindiga sun kuma bankawa motoci biyu wuta.

To sai dai Sani Abdullahi mazaunin ƙauyen Gobirawa ya ce mutanen 19 ‘yan bindiga suka kashe, wasu da yawa sun samu munanan raunuka,wasu kuma har yanzu ba a iya gano su ba.

Sani ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda ‘yan bindigan suka kashe a ƙauyen mata ne da yara da tsofaffi.

“Yan bindigan sun koma gidaje fiye da 20 a ƙauyen Gobirawa” inji Sani mazaunin garin.

By ukarofi