
Daga BELLO A. BABAJI
Matatar Man Fetur ta Ɗangote ta ce tsarin cinikayyar ɗanyen mai da Naira na Shugaba Bola Tinubu ya taimaka musu wajen rage farashin fetur, lamarin da ya kai ga samun sauƙinsa a gidajen mai.
Kamfanin man ya ce, duk da hauhawar farashin mai a kasuwar mai a mataki na duniya, yana samun damar yin ragi akai-akai don tabbatar da samar da sauƙi ga al’umma.
A sanarwar da babban jami’in yaɗa labaran kamfanin, Anthony Chiejina ya fitar, ya ce hakan na samuwa ne a ƙoƙarinsu na tallafa wa Tattalin arziƙin Nijeriya da rage raďaďi ga kwastomomi duk da matsin ƙarin farashi da ɓangaren ke fuskanta.
Ya ce, suna yaba wa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarinsa na samar da tsarin cinikayyar da Naira don amfanin al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya kuma ce, su na ƙoƙarin ɗore wa aka samar da fetur mai inganci ga al’umma da dacewa da manufar Gwamnatin Tarayya na fifita kayayyakin da aka samar a gida akan na waje.
Haka kuma, ya ƙara da cewa kamfanin ya tabbatar wa masu-ruwa-da-tsaki da suka haɗa da kwastomomi da abokan hulďa da gwamnati cewa za ta cigaba da aiki tukuru wajen hidima ga ci-gaban ƙasa.
