Ruwan sama ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Mamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara da ke cikin Jihar Katsina.

Majiyoyi daga ƙaramar hukumar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda shaidun gani da ido ya bayyana cewar ruwan wanda aka kwashe sa’o’i fiye da 24 ana tafkawa ya kware kwanon rufin gidaje gami da rushewar wasu gidaje da yawa.

Manhaja ta samu labarin cewar lamarin ya fi shafar garuruwan Nasarawa, Tsiga da kuma  mazauna garin na Ƙanƙara.

Mai magana da yawun ƙaramar hukumar Malam Abdulkarim Sani ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai inda ya bayyana cewar ibtila’i ne daga Indallahi.

Haka zalika hukumar bada agajin gaggawa ta jihar wato SEMA ta tabbatar da faruwar lamarin inda jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar ya ce hukumar za ta ziyarci wurin da lamarin ya faru domin ƙididdige iya ɓarnar da aka samu.

Tuni dai aka yi jana’izar waɗanda suka rasa rayukansu kamar yadda addinin Musulunci ya shar’anta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *