Muna cikin matsala a APC idan ba mu zaɓi tikitin takarar Musulmi da Musulmi ba – Kalu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa, hanya ɗaya tilo da zai kai ga samun nasara ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya ɗauko mataimaki Musulmi daga Arewa, ya ce, sancewar matarsa, Oluremi Tinubu za ta raba gardamar taƙaddamar da ake yi kan ɗaukar Musulmi a matsayin mataimaki kasancewarta Fasto.

Siyasar dai ta yi zafi ne kan yiwuwar samun tikitin tsayawa takarar Musulmi da Musulmi a jam’iyyar APC mai mulki.

Kalu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wata tattaunawa da manema labarai a gaban zauren majalisar.

Ya ƙara da cewa, Tinubu a matsayinsa na ’yan tsiraru Musulmi daga Kudu ba zai iya ɗaukar ’yan tsirarun Kiristoci daga Arewa ba.

Sai dai Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta gargaɗi manyan jam’iyyun ƙasar nan kan bai wa mabiya addini ɗaya tikitin takarar.

Amma wasu masu ruwa da tsaki sun buƙaci ’yan Nijeriya da su mai da hankali kan cancanta fiye da bambamcin addini.

Orji Kalu, ya buqaci Kiristoci da kada su ji tsoro tun da matar Tinubun Fasto ce.

“Bari na faɗa muku, a gidana, matata ce shugabar gidan a zahiri. Ko ku mazan da suke nan, yanzu da matanku ba sa nan, su ne shugabannin gidan. Matarka ce za ta baka damar saka kayan da suka dace da kai.

“Matarka za ta ce maka ga abin da ya kamata ka ci; koko ko ƙosai. Ko ka yi gardama daga ƙarshe zaɓinta za ka bi, kuma idan ta ce a biya kuɗin makarantar yara haka za ka biya babu jayayya.

“Ya kamata Kiristoci su kwantar da hankalinsu domin matar Tinubu fasto ce, za mu samu kariya. Tana da ilimin siyasa,” inji shi.

Matar Tinubu, wacce a halin yanzu ke wakiltar Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, an naɗa ta a matsayin Mataimakiyar Fasto ta cocin RCCG a 2018.

Ɗan takarar Shugaban ƙasar na APC na daga cikin waɗanda suka halarci bikin naɗin nata.