Shaka Zulu: Tushen al’ummar Zulu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sunan Shaka Zulu na da nasaba da yaƙi. Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba.

Kafin a haifi Shaka, wata bokanya mai suna Sithayi, ta ba da labarin cewa za a haifi wani yaro wanda zai kawo sabon sauyi da kuma sabuwar ƙasa. Ya kasance soja ɗan baiwa a Afirka. Mutum ne wanda ya gina ƙasa ba mai son kisa da zubar da jini ba. Kuma ba mutum ne mara tausayi ɗan ina da kisa ba.

An haifi shi a watan Juli shekarar 1787 a cikin al’ummar eLangeni inda mahaifiyarsa ta fito.

Mahaifinsa mutum ne mai aiki da hankali (Senzangakhona). Mahaifiyarsa ‘yar sarkin Nandi ce a gidan sarautar Mhlongo wanda ya rayu a wurin da ake kira eLangeni. Sunan Shaka ya samo asali ne daga wata cuta da ake kira Ishaka. Wannan cuta na sanya jikin mata ya riƙa ciwo da kasala da kuma kumburi. A lokacin da mahaifiyarsa wadda a wancan lokaci ba ta yi aure ba ta samu ciki, mutane sun yi tsammanin tana fama ne da cutar Ishaka. Yadda Shaka ya sami wannan sunan kenan.

Saboda haka ya kasance Shaka ɗan Senzangakhona. A wancan lokaci sunan mahaifinka shi ne sunanka na biyu. Kuma sunan kakan Shaka shi ne Zulu. Lokacin da Zulu ya zama sarki, sai Shaka ya ce ya kamata mu sami al’adarmu mu kira kanmu mutanen Zulu. Shi ne na farko da ya kira jama’arsa mutane Zulu, shi ya sa aka san shi a matsayin wanda ya kafa ƙasar Zulu duk da cewa ya gaji sarautar da ta daɗe tsawon zamani.

Ya yi ta ƙoƙarin musantawa saboda yana tsaron mahaifinsa, Sarki Zulu. Ga yarima mai jiran gadon sarauta kamar Senzangakhona ya yi wa yarinya ciki kafin aure abin kunya ne wanda ka iya kaiwa ga hukunci mai tsanani ciki har da yiwuwar rasa damar yin sarauta. Daga baya iyayensa suka amince kuma Senzangakhona ya biya kuyxin sadaki wanda ya bai wa Nandi damar tarewa cikin iyalan Senzangakhona.

Nandi mace ce mai ɗagawa da saurin fushi da so a kullum ta riƙa bai wa mutane umarni. A saboda haka dangantakarsu ta kasance cike da rigingimu. Senzangakhona ba zai iya jurewa ba. Ya kore ta tare da Shaka. Sun yi ta watangaririya. Nandi ta haɗu da Ngwati. Suka fara soyayya su ka cigaba da zama tare inda ta haifi ƙanwar Shaka.

Ya zama babban yaron Sarki Dingiswayo a lokacin da ya ke ɗan shekaru 16 da haihuwa. Wannan kuwa ya kasance ne saboda basirarsa da kuma ƙarfin zuciya. Ba a jima ba aka ɗauke shi a matsayin mayaƙi aka sa shi cikin rundunar Izicwe.

A matsayin kwamanda ya hana mayaƙan sanya takalmi faɗe ya kuma umarcesu su riƙa tafiya babu takalmi. Haka kuma ya hana amfani da dogon mashi wanda mayaƙa za su harbi abokin gama da shi. Maimakon haka, ya ɓullo da gajeren mashi ‘Iklwa’ domin faɗa daf-da-daf da abokin gaba. Wannan ya tilasta wa mayakansa su matso kusa su sari abokin gaba sannan su juya su sari wani da makami ɗaya. Ya kuma vullo da dabarar raba mayaƙa dama da hagu domin yi wa abokan gaba ƙofar rago. Tsarin ya yi kama da yanayin kahuna biyu na karkanda. Ya zama mutumin da ake matuƙar jin tsoronsa wanda kuma ya yi fice hatta a sauran ƙabilu da masarautu, a kan haka ne ma ya sami sunan ‘Nodumehleli’ wanda ke nufin wanda daga zaune ya ke sa duniya ta girgiza.

A lokacin da mahaifinsa Senzangakhona ya rasu, Sarki Dingiswayo ya taimaka masa dawowa wajen al’ummar mahaifinsa inda ya ba shi mayaƙa biyu su taimaka masa karɓe ragamar mulki. Sai dai Senzangakhona ya faɗa wa babban wazirinsa cewa ɗaya ɗan nasa Sigujana shi ne yarimansu mai jiran gado amma ba Shaka ba. Da isarsa sai ya kashe Sigujana kuma ya karɓi karagar mulki a shekarar 1816 a matsayin Sarki. Bayan mutuwar Sarki Dingiswayo, Shaka shigar da mutanen Mthethwa ƙarƙashin daularsa sannan ya ƙabilar da Dingiswayo ya ci da yaqi cikin sojojin da ke ƙarƙashin jagorancin Shaka. Ya kuma cigaba ya ci sauran ƙabilu da yaƙi ya kuma mulkesu.

Mummunan tunaninsa ga aure ya faru ne sakamakon yadda ya ga aka yi wa mahaifiyarsa. Sannan an ci zalinsa matuƙa sakamakon tasowa da ya yi ba cikin danginsa ba kuma ba tare da mahaifinsa ba. Babu shakka ya yi jima’i da mata to amma da zarar sun sami ciki sai ya miqa su ga ɗan uwansa, Mpande wanda ake gani a matsayin rauni.

Wannan tunani ne na ƙasashen yamma, kuma ba gaskiya ba ne. Ka tuna mutane miliyan 50 suka mutu a yaƙin duniya na biyu baya ga wasu miliyoyi da suka rasa rayukansu a yaƙin duniya na ɗaya. A saboda haka wane ne ya fi rashin imani tsakanin Shaka da waɗannan Turawa da suka haddasa yaƙin duniya na ɗaya da na biyu? To amma ya kamata a ɗauki kisan da aka aikata a wannan hali a yanayi na lokaci. Abu ne da mutane su ka saba da shi a wancan lokaci. Zai bada dalilai da su ka sa aka aikata kisan. Alal misali, waɗanda aka tabbatar da cewa mayu ne an kashe su. Sarakuna a wancan zamani sun ɗore ta hanyar kashe abokan hamayyarsu.

Zanen Shaka Zulu

An kashe shi a cikin watan Satumba shekarar 1828. Akwai wani makirci da aka shirya bisa jagorancin goggonsa. Babban dalili shi ne bayan mutuwar mahaifiyarsa Nandi, Shaka ya samu taɓin hankali inda ya kashe mutane da dama ba tare da yin tunani ba inda ya fake da jimamin mutuwar mahaifiyarsa. Wasu ya kashe su ne saboda sun ci zalinsa a lokacin da ya ke ɗan yaro, yayin da wasu kuma aka kashe su saboda ba su nuna alhini sosai game da rasuwar mahaifisarsa ba.

Gwarzon soja ne ɗan baiwa na Afirka. Me ya sa ba za a ce da Napoleon farin Shaka ba? Bai taɓa zuwa Turai ba kuma babu wani Bature da ya koyar da shi abubuwan da ya yi a fagen yaƙi. Sun fito ne daga baiwar da ya ke da ita.

Shi ne jigon haɗin kan Zulu. Jam’iyyar Inkatha Freedom Party wadda ta mamaye Kwazulu Natal ta danganta kanta da Sarki Shaka a matsayin tushenta. Sarakunan Zulu da al’ummarsu suna yin mubaya’a ga sarautar Sarki Shaka har zuwa yau.