Labarin Xi Jinping da mahaifinsa

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya ce “Ina fatan ƙara koyon kyawawan ɗabi’u masu daraja daga mahaifina”.

Mahaifinsa Xi Zhongxun, “wani jagoran al’umma ne wanda ya samo asali daga al’umma”. Ya kan ce shi da ne na manomi, wanda har kullum ya kan maida shi kansa a matsayin ɗaya daga cikin al’umma.

Duk wanda ke ƙaunar al’umma da samar musu da alheri, al’umma za su maida shi tamkar dan uwansu. Samo asali daga al’umma, da kuma sake dawowa cikin al’umma, shi ne ainihin buri na farko na Xi Jinping da na mahaifinsa.

A lokutan juyin juya hali daban-daban, Xi Zhongxun ya kan lura da al’umma sosai, yana dora muhimmanci kan ainihin muradunsu.
Dogara kan al’umma, da bauta musu, nauyi ne da Xi Jinping da mahaifinsa suka ɗauka tare.

Tun da aka shirya babban taro karo na 18 na wakilan jam’iyyar kwaminis mai mulkin ƙasar Sin, kawo yanzu, shugaba Xi Jinping ya yi tattaki zuwa wurare 14 masu fama da matsanancin talauci a ƙasar, ya gudanar da nazari kan ayyukan yaƙi da talauci sama da sau 50, inda ya sauke nauyin tarihi dake wuyansa, tun daga ganewa idanunsa ainihin talaucin da ake fama da shi, har zuwa ɗaukar matakai na zahiri don yaƙi da talaucin.

A ranar 25 ga watan Oktobar shekara ta 2017, a wajen cikakken zama na farko na kwamitin ƙoli karo na 19 na jam’iyyar kwaminis, Xi Jinping ya bayyana cewa: “Jam’iyyar kwaminis gami da al’umma, sun miƙa wannan babban aiki gare mu, saboda amincewa da kyakkyawan fatansu gare mu.

Bai kamata mu manta da burinmu tun farkon farawa ba, da sauke babban nauyinmu, mu yi aiki tukuru, don bauta wa jam’iyya gami da kasarmu baki ɗaya, da bayar da gudummawa wajen gina al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni, da samun nasarar raya ƙasa mai tsarin gurguzu irin na salon musamman a sabon zamanin da muke ciki.”

Fassrawa: Murtala Zhang