Daga AMINA YUSUF ALI
Barkarnmu da haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun jaridar Blueprint Manhaja, mai farin jini. Hausawa sun ce: ‘Idan an bi ta ɓarawo, sai a bi ta ma bi sawu’. Kusan koyaushe a ƙasar Hausa muna magana a kan yawaitar mutuwar aure a ƙasar Hausa. Ni kaina na sha rubutu a kan hakan, kuma na sha ƙorafi daga ‘yanuwa maza masu kiran waya. Musamman masu ganin ina ɗaukar laifin rabuwar aure ina ɗora musu kacokan.
Duk da dai masu bibiyar shafin nan sun shaida cewa, kowanne lokaci mukan yi ƙoƙarin ganin mun taɓo kowanne ɓangare, na maza da mata. Domin a samu daidaito wanda shi ne fatanmu. Don haka yau mun waiwayi mata. A sha karatu lafiya.
Da farko dai kamar yadda aka sani, kusan kowacce mace ta fi ɗora alhakin rabuwar mutuwar aure a kan namiji. Hakan wataƙila ba ya rasa nasaba da kasancewar igiyoyin numfashin auren yana tafukan hannayen mazan. Kuma yana da ikon iya tsittsinka igiyoyin, ko ya yi musu ƙamshin mutuwa a duk sanda ya so, ya ƙarar da rayuwarsu. Haka kuma zai iya zaɓar ya lallava su, ya raya su izuwa lokacin da ya yi muradi. Ku duba fa wannan baiwa da karramawa da Allah ya yi wa namiji. Ya ara masa caya daga cikin damarmakinSa da siffofinSa na Rububiyya.
Wannan abu ya sa idan aka yi rabuwa, mata da yawa sun fi ba shi laifi. Duk da wasu lokutan an fi ganin mace a matsayin mai laifi. To amma abin dubawa idan namiji ya so aure ya zauna, zai zauna. Idan bai so ba, ba zai zauna ba, faƙat! Saboda al’ummarmu tana ganin mace idan an rabu ta fi namijin cutuwa, shi ya sa ba za a yi zaton za ta yi abinda auren zai rabu ba.
Amma fa Bahaushe ya yi magana fa da ya ce wai idan an bi ta ɓarawo, to a bi ta ma bi sawu. Kuma idan ɓera da sata, daddawa ma da wari. Kamar yadda mawaƙi Hamisu Yadudu yake cewa, “ba rabewa, yalo da ɗata. Masaƙar gwado, a nan ake saƙa shata”. Ma’ana ba a ɗora laifi a kan ɓangare guda. Duk yadda muke ganin mace ba ta da laifi a mutuwar aure, wata macen fa ita take ba da kaso ma fi tsoka na dalilin mutuwar auren.
Ga wasu jerin abubuwa da mata suke yi wanda ke tilasta rabuwar aure ta faru. Sai a kiyaye, mata. Ba kullum aure ya rabu ba ki ce an zalunce ki ba. Ke ma wani abin fa da halinki.
Na farko akwai rashin kamun kai. Musamman wacce nata ya yi ƙamari har take zina da wasu mazan a waje. Gaskiya babu namijin kirki, kai ko ba na kirki ba wanda matarsa za ta dinga bin maza ko neman mata, yana ji da kallo ya ƙi rabuwa da ita.
Na biyu, raini da zagin iyayensa. Da wahala a ce namiji ɗan albarka kuma ɗan halas ya zauna da mace tana raina masa iyaye ko cin mutuncinsu ba. Zamani ya kawo mu, mace tana kishi da surukai. Wata har rashin kunya da zagi. Don haka mai wannan halin idan aka sake ki kada ki zargi kowa sai kanki.
Na uku, rashin yi wa miji biyayya. Idan mace ba ta wa miji biyayya, da wuya ya iya zama da ita. Bai isa ya sa ko ya hana ki ba, akwai matsala. Ba namijin da zai zauna da macen da ba ta girmama shi.
Na huɗu, surukai marasa kirki. Idan iyayen mace ƙananan mutane ne, suna zubar wa da ‘yarsu mutunci ta hanyar shiga harkar gidan mijin, gaskiya tamkar sun nema wa ‘yarsu tikitin zama bazawara ne. Don ba inda auren zai je. Ba namijin da zai yarda.
Na biyar, mace ta dinga hana namiji haƙƙoƙinsa na shari’a da suka rataya a wuyanta. Wata ba za ta yi masa girki ba, ko ta dinga ƙin saurarensa lokacin da ya neme ta, da sauran abubuwa. Ko ta ƙi tambayar sa idan za ta fita. Wannan ma da wuya namiji ya zauna da mai wannan halin.
Na shidda, akwai mace mai ɓata tarbiyya. Wata macen sai an auro ta ana zaune da ita, sai ta ɓullo da wasu halayen da shi mijin zai ji tsoron kada yaranta su kwaikwaye ta su dinga yi. Domin dole suna tare da yaran koyaushe. Uwa ita ce makarantar koyo ta farko ga yaranta. Duk abinda take yi, shi za su yi. Wani namijin zai ga kawai rabuwa da ita ne kawai mafita don kada ta lalata masa yara.
Na shida, gano sirrin ɓoye. Kwanakin baya na ji wani labari wanda ya cika Duniya na wani mutum da ya saki matarsa bayan daren farkonsu, inda ya gano ta ha’ince shi ta hanyar yin ciko a jikinta. Shi kuma ya aura a rashin sani. Gaskiya wannan miji ya sha tofin Allah tsine wajen mutane. Amma ni Allah ya sani laifin yarinyar da aka saki na gani, ba nasa ba. Domin ban ga hujjar da za ki yi ciko don wani ya so ki ba. Idan kika zauna a hakan ma za ki samu wanda zai so ki a yadda kike. Shi kuma irin matar da yake ra’ayi kenan.
Kuma kada mu manta aure yarjejeniya ce. Kuma ana ƙulla shi kamar yadda ake ƙulla dukkan wata kwangila ta Duniya ko ciniki. To ina da tambaya, idan aka ƙulla ciniki aka gano akwai ha’inci ba warware shi ake yi ba? To shi ma haka auren. Sannan kuma wasu har rashin lafiya da lalurori suke ɓoye wa miji ko wasu sirrikan. Kamar a ce tana da yara a wani gidan, ko ta tava aure da sauransu. Duk ranar da ya gano waɗannan sirrikan, da wahala ya cigaba da zama da ita. Bayan ta yi masa gagarumar cin amana. Ko ba su rabu ba, zaman lafiya da yarda sun ƙare har abada. Saboda kullum zai kasance a zargin za ta ha’ince shi. Kuma zargi yana daga manyan dalilan da suke kashe aure.
Sai na bakwai, auren dole. Mata suna suka tara. Wata idan aka aura mata namiji ko ba ta so, saboda biyayyar iyaye takan zauna. Amma wata za ta yi ta nuna masa tsana da ƙiyayya har sai ya haƙura ya sake ta.
Na takwas, wata kuma matar da kanta da kanta za ta dinga neman sakin. Wata har cewa take idan ya haifu a cikin uwarsa ya sake ta. Kuma wata fa kawai ba sakin take so ba, kawai laifi ya yi mata take so ta nuna fushi. Sai dai idan ba a yi sa’a ba, auren nan sai ya mutu. Don zuciya ba ta da ƙashi.
Na tara, saka miji a kwana. Wasu matan Allah ya yi su da iya saka miji a kwana. Laifi kaɗan ta ce zavi ko ni ko kishiyata. Ko ta ce ya zaɓi ko ita ko danginsa ko makamancin haka. Wallahi kada ki fara don wataran za ki yi sara a kan gaɓa ya ce ba ke ɗin ya zaɓa ba. Ya za ki yi? Don haka da muguwar rawa gwamma ƙin tashi, ‘yaruwa.
Na bakwai, auren kisan wuta. Wata da ma takan yi aure da nufin ta fita ta koma gidan tsohon mijinta da ya yi mata saki uku. Wanda ba dama ta koma sai ta auri wani ya sake ta tukunna. Sai ka ga an yi aure amma mace ta yi ta uzzura wa mijinta sai ya sake ta. Don kawai ta koma gidan wani.
Na takwas, rashin son zaman lafiya. Wata macen Allah ya yi ta futinanniya ba ta son zaman lafiya. Duk ta bi ta rikita namiji ya ji duk Duniya idan ba sakinta ya yi ba ba zai ji daɗi ba. Idan kishiya gare ta, ta ƙi zaman lafiya da ita. Wata ma har da zaluntar yaran miji da uwarsu ta fita ko ta mutu.
Na tara, rabuwar kotu. Wata macen da kanta za ta kai ƙarar mijinta kotu domin a raba aurensu saboda ba ta son cigaba da zama da shi. Alqali kan duba yiwuwar sasanci tsakaninta da mijinta. Idan ba zai yiwu ba, to dole a raba auren.
Na goma sata da maita. Maganar Allah ba namijin da zai zauna da mace mai irin waɗannan halayen. Mace kamar ɓera komai ka ajiye sai dai ka dawo ka tarar da filinsa? Idan tana da kishiyoyi haka za ta yi ta yi musu ɗauke-cauke. Wani sa’in har a maƙwabta da dangin sai ta sayar da can hali. Wata da na sani har wajen ‘Yansanda ake zuwa mijin ya yi ta zaryar zuwa belinta. To a ƙarshe kuma ba kowa zai iya yin wannan rayuwar tozarci ba, dole ya sallame ta, ya shaƙi iskar ‘yanci.
.
Na ƙarshe, Halayyar namiji. Kowanne namiji akwai abinda ba zai jure ba na daga halayyar mata. Yadda halayyar ɗan adam take da ma akwai irin haka. Sai dai mazan sun banbanta kowa da abinda ya fi damun sa. Wani rashin iya magana, rashin iya girki da tsafta, wani yawo, rashin kulawa da gida da kanta, da sauransu. Amma yawanci ba halayen ke jawo saki ba illa, rashin biyayya ga umarninsa. Domin maza da yawa suna yi wa mace uzuri gami da fatan za ta gyara. Idan ba ta gyara ba na tsahon lokaci, to kuwa mijin zai iy sakinta don bakinsa ma ya huta. Kuma ko ba a rabun ba, za ta fice a ransa, sun daina faranta ran juna sai su yi ta zaman doya da manja. Ko sai ya ƙaro aure sannan zai samu lafiya. Ita kuma lokacin za ta tsiri yin gyaran. Amma idan ta yi rashin sa’a kuma ta makara.
Da waɗannan bayanai nake kiran mata da su gyara su kiyaye waɗannan abubuwa da za su iya jawo rabuwar aure. Ko ba don komai ba, sai don ita ce ta fi cutuwa da yaranta bayan rabuwar aure. Duk da mazan su ma abin yana taɓa su, amma su sai an ɗebi lokaci kafin nadama ta riske su.
Ina godiya ga masu kiran waya, da ba da shawara, da tsokaci da yabawa. Kuna ƙarfafa ta a kullum. Na gode.