Shiru-shiru ba tsoro ba ne…

Daga IBRAHIM YAYA

A duk lokacin da aka kira taruka kama daga na tattalin arziki, al’adu, ko wasanni ko Ilimi ko kare muhalli ko harkar tsaro, walau a mataki na ƙasa ko shiyya ko ƙasa da ƙasa, muhimman abubuwan da mahalarta tarukan ke tattaunawa, su ne matsaloli da nasarori da aka cimma a waɗannan fannoni, gami da sabbin dabaru ko matakai da aka bijiro da su don inganta su, wadda daga ƙarshe za su taimaka wajen haifar da kyakkyawan sakamako da ma burin da ake fatan cimmawa, wanda zai amfani duniya baki ɗaya.

Sai dai wani abin mamaki shi ne, yayin taron tsaro na Shangri-La karo na 19 da ya gudana a ƙasar Singapore, maimakon a mayar da hankali kan yadda za a inganta matakan tsaro da zai amfani duniya baki ɗaya, sai Amurka da wasu kawayenta suka mayar da hankali kawai wajen neman shafawa ƙasar Sin baƙin fenti da ma tsoma baki a harkokin cikin gidanta. Wannan ya sa ministan tsaron ƙasar Sin Wei Fenghe, yayin da yake gabatar da nasa jawabin a wajen taron, ya nunawa masu irin wannan mugun nufi kan ƙasar Sin cewa, shiru-shiru fa ba tsoro ba ne…

Saƙon da minista Wei ya gabatar, ya ƙara tunatar da ɓangaren Amurka da ma duniya baki ɗaya cewa, yanzu hulɗar da ke tsakanin ƙasashen 2 tana cikin wani muhimmin lokaci, kuma kyakkyawar hulɗar da ke tsakaninta da Amurka ta dace da muradunsu da ma duniya baki ɗaya.

Amma idan har Amurka ta nace da neman tayar da rikici tsakaninta da Sin, to hakan ba zai kawo musu da ma ƙasashen duniya alheri ba. Haka kuma bai dace ba Amurka da ƙawayenta su rika ayyana ƙasar Sin a matsayin wai mai takara da Amurka ko barazana, idan kuma suka yi hakan, haƙiƙa za ta yi mummunan kuskure. Idan kunne ya ji, to gangan jiki ya tsira.

Ƙasar Sin dai ta buƙaci Amurka da ta daina shafa mata kashin kaji, da neman daƙile ci gaban ta, kana ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta, da kuma illanta muradun ƙasar Sin. Wani muhimmin batu da Amurka da sauran masu neman ballewar yankin Taiwan ya dace su fahimta da kunnen basira shi ne, sake haɗewar Taiwan da babban yanki cikin lumana, shi ne babban fatan al’ummar Sinawa. Kuma duk wanda ya kuskura ya nemi tayar da batun ɓallewar yankin Taiwan daga ƙasar Sin, ƙasar Sin ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen mayar da duk wani martani ko ta halin kaka. Domin yaro bai san wuta ba, sai ya taka.

Masu fashin baki na ƙara jaddada cewa, wajibi ne Sin da Amurka su tattauna da juna, su mutunta juna, su kuma zauna tare cikin lumana, su haɗa kansu domin samun moriyar juna, amma idan Amurka ta nemi yin fito-na-fito da Sin, to, ƙasar Sin ta sha nanata cewa, ba za ta yarda a yi mata sakiyar da babu ruwa ba.