Xi Jinping ya tattauna da Putin ta wayar tarho

Daga CMG HAUSA

A yammacin yau ne, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na ƙasar Rasha Vladimir Putin.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, ƙasar Sin na son hada kai tare da ƙasar Rasha, wajen inganta hadin gwiwarsu ta hanyar da ta dace. Ƙasar Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga ƙasar Rasha kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu, da manyan batutuwan da suka shafi harkokin ikon mulkin ƙasa, da tsaro, da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin ƙasashen biyu, da ƙarfafa tattaunawa da yin haɗin gwiwa a tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na shiyya-shiyya kamar MƊD, da ƙasashen BRICS da ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai, da sa kaimi ga bunƙasuwar tsarin ƙasa da ƙasa da tafiyar da harkokin duniya bisa tsari na gaskiya da adalci.

A nasa jawabin, shugaba Putin ya bayhana cewa, ƙasar Rasha na goyon bayan shawarar ƙasar Sin kan tsaron ƙasa da ƙasa, kuma tana adawa da duk wani yunkuri na neman tsoma baki a harkokin cikin gidan ƙasar Sin ta hanyar fakewa da batun Xinjiang, da Hong Kong da kuma yankin Taiwan. Ƙasar Rasha na son karfafa haɗin gwiwar ɓangarori daban-daban tare da ƙasar Sin, da yin ƙoƙarin da ya dace don bunƙasa duniya mai kunshe da kowa, da kafa tsarin ƙasa da ƙasa mai adalci da ma’ana.

Haka kuma, shugabannin kasashen biyu, sun yi musayar ra’ ayi kan batun ƙasar Ukraine. Shugaba Xi ya ƙara da cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana ci gaba da tafiya ne kan batun da ya shafi tarihi da kuma cancanta game da batun Ukraine, da yanke hukunci mai zaman kansa, da sa ƙaimi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsarin tattalin arzikin duniya. Don haka, ya kamata dukkan ɓangarori su matsa ƙaimin wajen warware rikicin ƙasar Ukarine bisa gaskiya. Ƙasar Sin tana son ci gaba da taka rawar da ta dace a wannan fanni.

Fassarawa: Ibrahim