Yaushe Amurka za ta cika alƙawarin da ta yiwa ƙasar Sin?

Daga CMG HAUSA

Mamban hukumar siyasar kwamitin ƙolin JKS kuma darektan ofishin hukumar kula da harkokin waje ta kwamitin Yang Jiechi ya gana da mai taimakawa shugaban ƙasar Amurka kan tsaron ƙasa Jake Sullivan a Luxembourg a Litinin da ta gabata har na tsawon awoyi huɗu, inda suka yi tattaunawa mai zurfi, tare kuma da amincewa da tabbatar da matsaya guda da shugabannin ƙasashen biyu wato Sin da Amurka suka cimma.

Yanzu hulɗar dake tsakanin sassan biyu ta gamu da matsala, sakamakon ƙasa tabbatar da matsayar da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma, duk da cewa, ƙasar Sin ta nuna sahihanci kuma ta himmantu matuka kan aikin.

An lura cewa, ba zai yiyu a kyautata hulɗar dake tsakanin Sin da Amurka bisa ƙoƙarin da ƙasar Sin take yi ita kaɗai ba, yanzu haka Amurka wadda ta saba da tunanin nuna fin karfi tana lalata hulɗar ta hanyar da take so.

Kwanan baya tsohon sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka mai shekaru 99 Henry Kissinger ya zanta da manema labaran jaridar “The Sunday Times”, inda ya bayyana cewa, bai kamata Amurka ta bukaci ƙasar Sin ta dace da ma’auni ko al’adu na ƙasashen yamma ba, abu mafi muhimmanci yayin da ake ƙoƙarin raya huldar dake tsakanin Sin da Amurka shi ne, tabbatar da matsaya guda da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma. Kuma abun da ya fi jan hankulan al’ummun ƙasa da ƙasa shi ne, yaushe Amurka za ta cika alƙawarin da ta yiwa ƙasar Sin wato ba za ta yi yakin cacar baka, da sauya tsarin ƙasar Sin, da adawa da ƙasar Sin, da goyon bayan ‘yancin kan Taiwan, da kuma tayar da rikicin dake tsakaninta da ƙasar Sin ba.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa