Sin: An ƙaddamar da jarrabawar shiga jami’a

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Yau Talata ne aka fara gudanar da jarrabawar shiga jami’a a sassa daban daban na ƙasar Sin.

Alƙaluman ma’aikatar ilmi ta ƙasar Sin sun nuna cewa, yawan waɗanda suka yi rajistar rubuta jarrabawar a bana ya kafa tarihi, inda ya kai miliyan 11.93 baki ɗaya, wanda ya ƙaru da miliyan 1 da dubu 150 bisa na shekarar 2021.

Akwai wuraren gudanar da jarrabawar guda dubu 330 a duk fadin ƙasar Sin, tare da masu sa ido kimanin miliyan 1 da dubu 20.

Fassarawa: Tasallah Yuan

By Editor