Rahoton EU game da Hong Kong na cike da yaudara

Spread the love

Daga FAEZA MUSTAPHA

Har kullum ƙasashen yammacin duniya na nacewa manufofin nuna yatsa ga ƙasar Sin, ta hanyar fakewa da yayata dimokaraɗiyya, ko kare haƙƙin bil adama, duk kuwa da irin nasu tarin matsalolin na cikin gida.

A baya bayan nan, wani rahoto da Tarayyar Turai EU ta fitar mai taken “Rahoton shekara game da yankin musamman na Hong Kong na shekarar 2021”, ya ƙunshi bayanai masu tarin yawa, da EUn ke iƙirarin haka ya kamata ƙasar Sin ta rika tafiyar da harkoki a yankin na HK.

Wannan rahoto, wanda shi ne irinsa na 24 da EUn ta fitar, na ƙunshe da kalamai na yaudara da suka saba da gaskiya, ciki har da zargin wai “yanayin kare haƙƙin bil adama na kara taɓarɓarewa a yankin na HK”.

Amma abun tambaya a nan shi ne, ko Tarayyar Turai EU, ta taba fitar da makamancin wannan rahoto game da HK cikin shekaru sama da 140 da Birtaniya ta mulkin yankin, ƙarƙashin mulkin danniya da watsi da dimokaraɗiyya?

Idan da a ce ƙasar Sin ce ta fitar da makamancin wannan rahoto, game da buƙatar gyara yanayin gudanar da mulki a Turai, da magance matsalolin dake yawan haifar da zanga-zanga, da fito-na-fito da mahukunta a Turai, da gazawar gwamnatocin Turai wajen shawo kan annoba yadda ya kamata, manya ƙasashe mambobin EU za su yi maraba da wannan rahoto?

Kowa ya sani cewa, a lokuta mabambanta, wasu daga ƙasashe mambobin ƙungiyar EU, sun fuskanci matsalolin tsaro makamantan waɗanda Sin ta fuskanta a yankin musamman na HK. Ga misali, ƙasar Faransa ta sha fama da zanga zanga da fito-na-fito sakamakon dalilai na siyasa, tun daga watan Nuwamban shekarar 2018.

Ya zuwa tsakiyar shekarar 2019, tashe-tashen hankula sun haifar da rasuwar mutane 11, da jikkatar fararen hula 2,500, baya ga jami’an tsaro 1,800 da su ma suka jikkata. Kaza lika an cafke adadin mutane da yawansu ya kai sama da 8,000.

Rahotanni sun ce an yi amfani da ƙarfin tuwo wajen tabbatar da doka da oda. Inda mahukuntan Faransa suka rika barazanar ɗaukar matakan ba-sani-ba-sabo kan masu tayar da ƙayar baya.

Sai dai abun mamaki a nan shi ne, da yawa daga kafofin watsa labaran ƙasar Faransa, sun rika kiran ɓarnata gine-gine da masu zanga-zangar suka yi a birnin Paris a wancan lokaci, da aikin tsageru, amma a ɗaya hannun, sun rika kiran matakin lalata zauren majalisar dokokin yankin HK da masu zanga-zanga suka yi da “jarunta” shin wannan ba nuna fuska biyu ba ne?

Amfani da irin wannan mizani 2 wajen kwatanta abubuwa makamantan juna, da wariya, da kauce wa adalci daga gwamnatoci da kafafen watsa labaran ƙasashen yamma suke yi, ya yi daidai da karin maganar Bahaushe dake cewa “Laifi tudu ne, ka take naka ka hango na wani”.

Har kullum, sassa daban daban na ƙasashen yammacin duniya na yawan maimaita muhimmancin kare haƙƙin bil adama. Amma sun mance cewa, lullube laifukan da suke aikatawa na keta haƙƙin bil adama, da kokarin ganin baiken ƙasar Sin kan haƙƙin bil adama, yana kara fallasa aniyar su ta siyasantar da batun haƙƙin bil adama. Kuma irin waɗannan rahotanni masu cike da ƙage, da rashin adalci da EU ke fitarwa, ba za su sauya hakikanin gaskiyar da dukkanin al’ummun duniya suka sani ba.

By Editor