Alƙaluma sun bayyana a zahiri

Spread the love

Daga LUBABATU LEI

Kwanan nan, babbar kwamishinar MƊD mai kula da harkokin haƙƙin bil Adam Madam Michelle Bachelet ta kawo karshen ziyararta a kasar Sin. A gun taron manema labarai da aka gudanar, Madam Bachelet ta bayyana abubuwan da ta gani da idonta a yayin ziyarar, inda ta jaddada cewa, ta tuntubi sassa daban daban ba tare da an sanya mata ido ba, furucin da ya karyata jita-jitar da ‘yan siyasar Amurka da na ƙasashen yamma suke kokarin yadawa dangane da Xinjiang, waɗanda har suka bukace ta da yi murabus daga mukaminta.

Shafawa ƙasar Sin bakin fenti bisa wai “batun Xinjiang” don neman daƙile ci gaban kasar, ba wani boyayyen abu ba ne ga Amurka da kawayenta. Rahoton na cewa, jami’an karamin ofishin jakadancin Amurka a birnin Guangzhou na ƙasar Sin, Sheila Carey da Andrew Chira, sun bayyana wa baki a wata liyafa a shekarar 2021 cewa, gwamnatin Amurka tana fatan ‘yan kasuwan Amurka su fahimci cewa, batun aikin tilas da na kisan ƙare dangi da ake yayatawa kan jihar Xinjiang, “mataki ne da ya dace” a yunkurin da ake yi na “jefa gwamnatin ƙasar Sin cikin mawuyacin hali.”

Shi ma Lawrence Wilkerson, babban jami’in tsohuwar gwamnatin Amurka ya bayyana a shekarar 2018 cewa, mataki mafi kyau ga Amurka wajen lahanta kwanciyar hankalin ƙasar Sin, shi ne tada zaune-tsaye a jihar Xinjiang, don kawo wa ƙasar matsala a cikin gidanta.

“Tilasta wa ‘yan ƙabilar Uygur yin aiki” da “yi musu kisan ƙare dangi”, laifuffuka ne da Amurka da kawayenta suka dora wa ƙasar Sin, amma karya fure take ba ta ‘ya’ya. Cikin shekaru sama da 70 da suka wuce, yawan ‘yan ƙabilar Uygur mazauna jihar Xinjiang ya ƙaru daga miliyan 3.6 zuwa miliyan 11.6, kwatankwacin yadda Indiyawan daji ‘yan asalin Amurka suka ragu matuka cikin shekaru 400 da suka wuce, daga miliyan 5 zuwa dubu 250 a farkon karni na 20.

Mene ne gaskiyar lamarin? To, alƙaluma sun bayyana a zahiri.
Ƙasar da ta zo ta farko wajen yawan mamata a sanadin annobar Covid-19, wadda kuma ke fama da yawan harbe-harben bindiga da matsalar bambancin launin fata, muna ba ta shawarar mai da hankali a kan matsalar cikin gidanta maimakon shafawa wasu bakin fenti.

Mai Zane: Mustapha Bulama

By Editor