‘Yan bindiga sun sako mahaifiyar ɗan takarar sanatan Kano

Daga WAKILINMU

Bayanan da Manhaja ta samu na nuni da cewa, ‘yan bindiga sun sako mahaifiyar ɗan takarar sanata a Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin APC, Abdussalam Abdulkarim AA Zaura, wadda aka yi garkuwa da ita ta kuma tuni ta haɗu da danginta.

An sace dattijiyar mai suna Hajiya Laure Mai Kunu ne da safiyar Litinin a gidanta da ke garin Zaura cikin ƙaramar hukumar Ungogo a Jihar Kano.

Wasu ‘yan bindiga su uku da ba a san ko su wane ne ba, su ne suka sace ta wanda daga bisani suka kira ahalinta suka faɗa musu cewa suna Jihar Katsina.

Sai dai, kwana ɗaya da ba da sanarwar sace dattijiyar da Shugaban Ƙaramar, Abdullahi Garba Ramat ya yi, sai aka ga an sako tsohuwar.

Shugaban hukumar ya wallafa a shafinsa na facebook cewa, “Alhamdu lillah, an kuɓutar da Hajiya Laure, mahaifiyar AA Zaura wadda aka yi garkuwa da ita lami lafiya.”

Haka shi ma ɗanta AA Zaura, ya tabbatar da sakin mahaifiyar tasa a shafinsa na facebook tare da nuna godiya ga jama’a da jami’an tsaro.

“Ina godiya ga hukumar DSS, Sojojin Sama, ‘yan sanda da jami’an tsaro na Civil Defense dangane da rawar da suka taka wajen kuɓutar da mahaifiyata.

“Ba zan taɓa daina kyawawan ayyukan da nake yi wa Kano ba. Na yi imanin cewa a matsayinsa na Musulmi, dole in fuskanci jarrabawa ta hanyoyi da dama,” inji shi.

Sai dai, babu wani cikakken bayani a kan ko sai da aka biya kuɗin fansa kafin aka sako dattiyar da lamarin ya shafa.