Martanin gwamnati ga Tinubu: ’Yan Nijeriya ne suka ɗora Buhari kan mulki ba kai ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, miliyoyin ’yan Nijeriya ne suka zaɓi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a zaɓen 2015.

A cewar fadar shugaban ƙasa, babu wani mutum ɗaya da zai iya cewa shi ne ya ɗauki nauyin zaman Buhari shugaban ƙasa.

Kalaman na zuwa ne a kan kalaman Bola Ahmed Tinubu, jigo a jam’iyyar APC na ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ranar Alhamis, 2 ga Yuni, 2022 a Abeokuta, jihar Ogun.

Tinubu ya ce, “ba don ni ba, da Buhari bai tsaya ba, da bai zama shugaban ƙasa ba. Ya gwada a karo na farko, ya kasa, na biyu, ya kasa, na uku, ya kasa. Ko da ya yi kuka a gidan talabijin na ƙasa ya sha alwashin ba zai ƙara tsayawa takara ba amma na je na same shi a Kaduna na ce masa zai sake tsayawa takara; Ni zan tsaya masa kuma zai yi nasara, amma kada ya yi wasa da Yarbawa kuma ya amince da su.”

A wata sanarwa da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga Buhari ya fitar a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, 2022, fadar shugaban ƙasar ta ce, mutane da dama sun taka rawa, manya da ƙanana a zaɓen 2015.

A halin da ake ciki kuma, Tinubu ya fitar da wata sanarwa a baya inda ya ce, kalamansa ba za su taɓa cin mutuncin shugaban ƙasa ba, inda ya ƙara da cewa, ya faɗi hakan ne kawai da fatan hakan zai gamsar da shugaban ƙasar wajen adawa da burinsa na zaɓen fidda gwani na jam’iyya mai mulki da za a yi a ranar 6 ga watan Yuni zuwa 8 ga watan Yuni, 2022.