Oba Ewuare: Basaraken Tagulla na birnin Benin

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Qasar Benin dai tana ɗaya daga ƙasashen yamma Afrika kuma ita ƙaramar ƙasa ce , da can ana ce ma ta Dukome. A shekara ta 1894  ƙasar Faransa ta mamaye ƙasar, zuwa shekara ta 1960 ta samu ’yancin kanta. Benin tana da iyaka da ƙasashe huɗu, su ne, daga gabacinta Nijeriya, daga yammacinta Togo, daga arewacinta Nijar, daga Arewa maso yammaci Burkina Faso.

Benin ƙasa ce me tsuwo daga kudanci zuwa arewaci (650 )km, kuma tsawanta daga gabarce zuwa yammace ( 110 ) km, harshen Faransanci shi ne yaren ƙasar, tana kuma da yawan mutane kimanin (4,418,000 ). A shekara ta 1988 babban birnin ta Cotono yawan mutanenta sun kai (1050). Benin tana da yaruka masu ɗumbin yawa kamar su, Fun, Adja, Buriya, Hausa, Dande da suran su.

Fiye da ƙarni biyar bayan sarautarsa, gadon da Oba Ewuare ya bari na nan daram a cikin garin Benin. Ana tunawa da ƙarfin ikonsa da kuma haɓaka fasahar sarrafa Tagulla da ake cin amfani har yanzu.

Oba Ewuare, wanda kuma aka sani da Oba Ewuare I ko Ewuare Mai Girma, ya jagoranci tsohuwar masarautar Benin daga 1440 zuwa 1473. Ya zama Sarkin Benin bayan ya yi amfani da ƙarfi wajen hamvarar da ɗan uwansa daga gadon sarauta. Wannan Juyin mulkin ya jefa birnin Benin cikin komabaya, amma ya sami damar sake gina garin, har ma ya maida shi abin da daga baya ya zama ɗaya daga cikin manyan daulolin da suka fi fice a Yammacin Afirka.

A zamanin mulkin Ewuare, an tsara babban birnin masarautar Benin yadda ya kamata, kuma yana ɗauke da adadi mai yawa na al’umma. An ce ya gina wasu ƙofofi tara na shigowa Benin city kuma ya kula da ginin hanyoyi da yawa. Labarai na baka waɗanda ba rubutattu ba, sun bayyana shi a matsayin babban matsafi, likita kuma jarumi.

Bunƙasar ayyukan fasaha a Benin ya kasance ɗaya daga cikin muhimman gado da ake tuna Oba Ewuare da shi. Ya gayyaci masana fasahar zane-zane da ƙere-ƙere na garin da su duƙufa wajen samar da fasaha mai inganci. Bugu da ƙari, ya ɓullo da ƙirar kawunan Tagulla don girmama sarakunan Benin da suka mutu. Sun kasance ƙere-ƙere masu matuƙar muhimmanci a cikin gidajen adana kayan tarihi a Nijeriya da kuma sassa na duniya. Haɓaka aikin fasaha da Ewuare ya yi ya haifar da kafa masana’antar sassaƙa hauren giwa da katako da Tagulla waɗanda har yanzu ake cin gajiyarsu.

Haka zalika Oba Ewuare ya yi shuhura wajen inganta ayyukan al’adun Benin. Ya gabatar da bikin Igue wanda ya kasance ɗaya daga cikin muhimman al’adun mutanen ƙasar Benin. Hakanan kuma, Oba Ewuare ya gabatar da murjani masu launin shuɗi a cikin Benin, waɗanda a yau suka zama kayan ado na sarauta da kuma al’adun gargajiyar Benin. A yau, amfani da murjani bai tsaya a masarautar Benin kawai ba. Amma ya bazu sosai zuwa sauran sassa na Kudancin Nijeriya – godiya ta tabbata ga Oba Ewuare da ya samar da wannan tsarin kwalliya.

Ewuare Babba ya kasance Oba na farko na Benin ba wai saboda shi ne farkon wanda ya fara mulkin masarautar Benin ba, amma saboda shi ne Oba na farko da ya sauya masarautar. Ya gaji ƙaramar masarauta amma ya faɗaɗa ta sosai inda ya haxa garuruwa da ƙauyuka da yawa. Matakan gudanarwa da ya fara ɗauka don tabbatar da miƙa mulki cikin lumana ya kasance abin da ake tunawa da shi har zuwa yau.  Kafa sharaɗin gadar mulkin da ya yi – ma’ana maye gurbi idan sarki ya rasu babban ɗansa ya gaje shi, ya kawo ƙarshen gwagwarmayar neman karve iko tsakanin ‘ya’yan sarki.

A shakarun baya da suka gabata, an samu labarin cewa wasu daga cikin Tagullar da ƙasar da ke ita an neme su sama da ƙasa babu su, amma a farkon shekarar nan an maido da tagulla biyu na masarautar gargajiyar Benin a Nijeriya, fiye da ƙarni ɗaya bayan da sojojin Birtaniya suka yi awon gaba da su, lamarin da ke ƙara sa rai cewa za a iya mayar da wasu dubban kayayyakin tarihi zuwa gidan kakanninsu.

Masu bincike da masu mulkin mallaka ne suka sace kayayyakin tarihin, galibi a Turai, daga Masarautar Benin, a yanzu kudu maso yammacin Nijeriya, kuma suna cikin manyan abubuwan tarihi na Afirka.

An ƙirƙire su a farkon ƙarni na 16, a cewar gidan kayan tarihi na Biritaniya.