2023: Gwamnonn APC sun miƙa wa Buhari sunayen ‘yan takara biyar

Daga BASHIR ISAH

Gwamnonin Jam’iyyar APC sun miƙa sunayen ‘yan takarar shugabancin ƙasa su biya ga Shugaba Muhammadu Buhari don ya zaɓi magajinsa daga cikinsu.

Majiyar Daily Trust ta bayyana cewa, gwamnonin sun miƙa sunayen ga Buharin ne a safiyar Talata.

Majiyar ta ƙara da cewa, sunayen da aka miqa ɗin sun haɗa da na Mataimakin Shuagaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, tsohon Gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi sai kuma sunan Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi.

Bayan ganawarsu da Buhari, gwamnonin sun ce za tafi su gana da uwar jam’iyyarsu kana su koma su sake ganawa da Shugaban Ƙasa.

Majiyarmu ta ce, gwamnonin sun ɗauki ɗan takara ɗaya daga Kudu maso Gabas, ɗaya daga Kudu maso Kudu, sannan uku daga Kudu maso Yamma wanda ya yi daidai da ra’ayinsu na son mulkin ƙasa ya koma Kudu.

A wannan Talatar ake ss ran APC ta gudanar da zaɓen fidda gwaninta.

Kafin wannan lokaci rahotann sun nuna Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nuna Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar da aka sasanta a kan takararsa, ra’ayin da tuni Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da shi.