Sojojin sun fatattaki ‘yan bindiga a Sakkwato da Zamfara

*An kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su

Daga BASHIR ISAH

Dakarun haɗin gwiwa na rundunar Hadarin Daji mai aikinta a jihohin Sakkwato, Katsina, Kebbi da Zamfara sun fatattaki ‘yan bindiga a maɓuyarsu da ke shiyyar Arewa maso Yamma tare da kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su.

Kazalika, sojoji sun ƙwace wasu kayayyaki daga ‘yan bindigar yayin samamen da suka haɗa da bindigogi da alburusai da babura da shanu da sauransu.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da Hedikwatar tsaro ta fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce a ranar 3 ga Agusta, sojoji sun daƙile yunƙurin harin ‘yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato, lamarin da ya sa maharan suka tsere ɗauke da raunukan harbin bindiga.

“Kazalika, dakarun runduna ta 8 sashen na 3 na Operation Hadarin Daji da ke aiki a Sabon Birni a Sakkwato, sun gano tare da lalata maɓuyar ‘yan ta’adda a dazukan Kusabunni da Tafkin Gawo da Alumdawa da Ungwar Mailele da kuma ƙauyen Malamawa” duk a Sakkwato in ji sanarwar.

Haka nan, samamen ya shafi wasu yankunan Jihar Katsina da suka haɗa da garin Kore cikin Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa, da Ungwan Madugu a Ƙaramar Hukumar Dandume.

Sojojin sun samu nasarar kuɓutar da wasu mutum 4 da ke hannun ‘yan bindigar waɗanda aka yi garkuwa da su a gona.

Rundunar ta ce tuni an sada waɗanda lamarin ya shafa da ahalinsu, haka ma an miƙa shanun da aka ƙwato wa masu su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *