Gwamnatin Filato ta rufe makarantu kan ɓarkewar cutar mashaƙo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Filato ta umarci a rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar, a matsayin ɓangare na matakin gaggawa domin rage cigaba da yaɗuwar cutar mashaƙo.

Rahotanni sun ce, umarnin na zuwa ne yayin da al’ummar jihar ke cigaba da fuskantar yaɗuwar rahoton cutar mashaƙo, inda a saboda haka ne hukumomin lafiya suka fitar da rahotannin cutar da waɗanda suka rasu a sanadiyyarta, musamman a Jos ta Arewa da wasu yankuna.

A wata sanarwa da Kwamishinar Yaɗa Labaran jihar, Joyce Ramnap ta fitar, ta ce umarnin zai fara aiki ne a ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, kuma ya ƙunshi makarantun da suka riga suka koma wa karatu. Gwamna Caleb Mutfwang acikin sanarwar, ya bayyana cewa an samu rahotannin yaɗuwar cutar a sassan jihar musamman a ƙananan hukumomin Jos ta Arewa, Wase, Jos ta Kudu da Bassa.

Gwamnatin ta bayyana cewa an ɗauki matakin rufe makarantun ne na wucin-gadi domin bayar da kariya ga lafiya da zaman lafiyar ɗalibai, malamai da sauran ma’aikatan makarantu yayin ƙoƙarin shawo kan annobar.

Akan haka ne aka buƙaci masu makarantu, jagorori da malamai da su yi biyayya ga umarnin yayin da ake sa ran iyaye su tabbatar da cewa ‘ya’yansu suna zama a gida a baki ɗaya lokacin. Sannan, gwamnatin ta roƙi masu ruwa da tsaki da su bayar da haɗin kai, tana mai cewa hakan na da nufin bayar da kariya ga yaɗuwar cutar a sassan jihar.

By Babaji

Leave a Reply