Taron ƙaddamar da littafin ‘Sirrin Mace Musulma’ ya ƙara farfaɗo da harkar adabin Hausa

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

A daidai lokacin da ake ganin harkar rubutun littattafan Hausa tana samun koma baya sakamakon yadda kasuwar littafin take durƙushewa sai ga shi ana samun wasu masu kishin Hausa da ci gaban adabin suna iya ƙoƙarin su domin ganin harkar ba ta kai ga durkushewa ba.

Fatima Aminu Alhassan Kabo tana ɗaya daga cikin mata da suka tsaya tare da jajircewa wajen samar da littattafai a wannan lokacin, bisa ƙoƙarin ta na samar da littafin da zai koyar tare da faɗakar da al’umma abin da ya shafi zamantakewar rayuwar aure musamman mata a wannan lokacin. Don haka ne ta yi namijin ƙoƙari wajen samar da littafin ‘Sirrin Mace Musulma’ domin bayar da gudunmawar ta ga al’umma.

A ranar Asabar 17 ga Mayu ne dai aka yi taron ƙaddamar da littafin na ‘Sirrin Mace Musulma’, wanda matashiyar marubuciya Fatima Aminu Alhassan Kabo ta wallafa.

Taron, wanda aka gudanar da shi a ƙofar fadar Hakimin Kabo, da ke ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano, ya samu mahalartar manyan baki kama daga ‘yan siyasa da sarakuna, malaman addini.

Tun da farko da yake ɗan taƙaitaccen bayani a wajen, babban bako mai jawabi, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON, ya yaba wa marubuciyar bisa ƙoƙarin ta na samar da littafin wanda a ganin sa a wannan lokacin ba ƙaramin ƙoƙari ta yi ba.

Domin a cewar sa ” Rubutun littattafai a yanzu sai wanda ya ɗaure kuma ya yarda sadaukarwa ne rubutun da ya yi domin bada gudunmawar sa.”

Don haka ya yi kira ga al’ummar da su daure su sayi littafin domin amfanuwar su ga abubuwan da littafin ya ƙunsa.

Haka nan ya yi kira ga ‘yan siyasar yankin na ƙaramar Hukumar Kabo da ma na Jihar Kano bakiɗaya da su ɗauki nauyin wallafa littafin da yawa domin raba wa ga makarantu, don ƙaruwar su da ilimin da ke cikin littafin.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙaramar Hukumar Kabo Honorabul Lawal Najumen Kano, wanda shi ne babban mai ƙaddamarwa, ya nuna farin cikin sa a game da samar da wannan littafin wanda kuma ya kasance marubuciyar ‘yar ƙaramar hukumar sa ce ta Kabo , don haka ya ƙara jinjina a gare ta tare da ba ta ƙwarin gwiwa don ganin ta ci gaba da samar da littattafai masu inganci don faɗakar da al’umma. Inda kuma daga nan ya ƙaddamar da sayen kwafin littafin a kan Naira miliyan ɗaya da rabi. Ya yin da Karamar Hukumar Kabo ta saya a kan kuɗi Naira miliyan ɗaya.

Sai kuma masu rufa masa baya, wakilin Sanata Barau Jibril, wakilin Hakimin Kabo, wakilin Honorabul Nasiru Sile Garo, wakilin Alhaji Fahad Adamu Dankabo, duk suka sayi nasu kwafin.

An dai tara kuɗi da kuma alƙawura masu yawa. Kuma Jama’a sun taru da dama a wajen.

Haka nan daga ɓangaren marubuta su ma taron ya samu halartar Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON, Sarkin Mawallafan Arewa tare da Sakataren ƙungiyar marubuta ta ƙasa (ANA) reshen Jihar Kano Ibrahim Muhammad Indabawa, Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka) da kuma Malama Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo

By ukarofi