Daga IBRAHIM MUHAMMAD INDABAWA
Sunan Littafi: Sirrin Mace Musulma
Marubuciya: Fatima Aminu Alhassan Kabo
Shekarar Bugawa: 2025
ISBN: 978-978-778-685-7
Maɗaba’a: AGF MULTIMEDIA
Yawan Shafuka: 226
Mai Nazari: Ibrahim Muhammad Indabawa
GABATARWA
Sirrin Mace Musulma littafi ne da marubuciyar ta rubuta shi don tunatar da jama’a musamman mata, dangane da muhimman haƙƙoƙin da suka rataya a wuyansu a rayuwarsu ta duniya. Ta tsara shi a bisa zubin babi-babi, wanda suka shafi ibada, mu’amala ko zamantakewa, kiwon lafiya, girke-girke da kuma koyon sana’o’i. Sannan sai ta ɗauki kowanne fanni ta yi wadataccen bayani a kai. Har ila yau marubuciyar ta ƙawata littafin da ƙwararan hujjoji daga Alƙur’ani mai girma da kuma hadisai. Misali, a shafi na 9, ‘…..ya ku mutane, haƙiƙa mu muka halicce ku daga namiji da mace…” (Surah Alhujrat, aya ta 13). Da kuma shafi na 10, ‘…ya ku waɗanda kuka yi imani, bai halatta ba a gareku, ku gaji mataye a kan tilas.” (Sura: Al-Nasa’I, aya ta 19), da shafi na 12, ‘…Haƙiƙa addinin addini a wajen Allah shi ne Musulunci.” (Suratul Ali-Imran, aya ta 19). da sauran wurare masu yawa.
Ta fara da kawo tarihin wace ce ma mace Musulma, wane ne Ubangijinta? Sannan mene ne addininta? A ƙasan kowace tambaya ta zo da gamsassun bayanai tare da hujjoji.
Abubuwan da kowanne bangare ya ƙunsa a taƙaice:
Ta fuskar babin ibada, marubuciyar ta yi ƙoƙari sosai wajen tunatar da mata matsayinsu a cikin addinin Musulunci, tare da kawo abubuwan da ya kamata su sani a cikin ibadarsu. Waɗannan abubuwa sun ƙunshi niyya, tuba, soyayya a Musulunci, tawakalli, haƙuri, godiya (ga Allah mahalicci da kuma abokin zama wato miji), fata, zuhudu da kuma abin da ya kasance halak da haram a gare su. A ƙarshen babin kuma ta kawo bayani dangane da ayyukan jiki. A iya wannan babi, mace za ta iya samun abubuwan da take buƙata wanda ya shafi addininta, don yin rayuwa mai kyau da dacewa.
A ɓangare Mu’amala kuwa, marubiyar ta yi ƙoƙari wajen fayyace tarbiyyar mace musulma, abin da ya shafi ƙawa ko ƙawayenta, suturar da ya kamata ‘ya mace musulma ta saka, tsaftar mace musamman ta fuskar gyaran jiki, rayuwar aure da tarbiyyar yara a musulunci, da kuma rayuwar mata gabaɗaya a wannan zamanin.
A babin kiwon lafiya, marubuciyar ta yi cikakken bayani dangane da abin da ya shafi ciwon sanyi da sirrin magungunan gargajiya. Maganin kowane ciwo, da kuma yadda ake amfani da shi. Kamar yadda za a gani idan an duba shafin.
Sai babi na gaba, wanda ya ƙunshi abinci. A cikinsa ne ta koyar da yadda ake yin abinci da abin sha iri-iri da sauran girke-girken zamani. Yadda ake haɗa kayan ƙamshi da kuma a irin abincin da ya kamata a yi amfani da kowanne daga cikinsu. A cikin wannan babi, marubuciyar ta ɗauki kowane abinci da ta kawo ɗaya bayan ɗaya ta yi bayanin yadda ake sarrafa shi da kuma kayan haɗin da ake buƙata don sarrafawa. Gamsasshen bayani, wanda zai iya gamsar da kowacce mace, ƙarama ko babba, saboda yadda ta yi bayani dalla-dalla yadda za a iya fahimta cikin sauƙi.
Sai babi na ƙarshe wato wanda yake magana a kan koyon sana’a. Kamar yadda sunan babin yake, an yi bayani ne a kan sana’o’in hannu da ya kamata kowacce mace ta koya don taimaka wa rayuwarta tun daga gidan iyayenta, har zuwa gidan mijinta.
A wannan ɓangare mai matuƙar muhimmanci, marubuciyar ta kawo sana’o’in da mata za su iya yi masu yawan gaske, amma wasu daga ciki su ne: Sabulu, garin sabulun wanki, turaren wuta da na jiki (humra), turaren sanya ɗaki ƙamshi (air freshner), man kitso, ƙunshi da dilka, ganyen shayi, kwalaca, man zafi dangin su rob da mansileta, mayukan shafawa iri daban-daban, yadda ake yin gugguro da kayan ƙwalam da maƙulashe (snacks) da sauransu.
Sannan ta ɗauki duk waɗannan sana’o’i ɗaya bayan ɗaya ta koyar da yadda ake haɗawa da kuma irin abubuwan da ake buƙata don haɗawa.
Bbabban jigon littafin: Babban jigon rubutun shi ne faɗakarwa ko tunatarwa a kan abin da ya shafi haƙƙoƙi da nauye-nauyen mace musulma a addinin Musulunci. Don haka, idan har an ɗauki littafin da niyyar samun ƙaruwa ta fuskar addini, to za a samu abubuwan ƙaruwa masu yawa da za su kasance kamar an je gaban malami ne don koya ko ɗaukar darasi.
ƙananan jigo: Sun ƙunshi kiwon lafiya, koyar da sana’o’i kuma koyar da girke-girke. Kamar yadda bayani ya zo a baya.
Abubuwa masu ƙayatarwa game da littafin:
Abubuwan birgewa a littafin suna da yawa, kuma su suka haɗu suka mayar da littafin na ƙwarai ga duk wanda ya ci karo da shi don karantawa. Amma wasu daga ciki sun haɗar da:
Ingancin Bugu: Haƙiƙa littafin ya samu ingantaccen aiki ta fuskar ɗab’i, wato daga bugawa shi zuwa haɗawa. Yadda ko makaho ne ya shafa shi zai fahimci haka daga riƙonsa.
Daidaitacciyar Hausa: Littafi ya samu gatan amfani da daidaitacciyar Hausa a wajen rubutunsa. Kasancewar akan yi rubutu ko littafi wanda zai iya samun inganci a wajen bugu, amma ka tarar cikinsa bai ƙunshi daidaitacciyar Hausa da ya kamata a yi rubutun Hausa da ita ba. Akwai misalin haka a shafi na
ƙa’idojin Rubutu: An bi dukkan ƙa’idojin da suka dace da rubutun Hausa ko na littafi, kamar yadda aka sani a rubutun zube ko na waƙoƙi da makamantansu. Waɗanda gazawarsu a cikin littafi ke sauya ma’anar abin da ake son isarwa gabaɗaya. Ba shakka a wannan fannin marubuciyar ta yi ƙoƙarin ganin ba ta bayar da wata ƙofa ta cin gyaranta a game da ƙa’idojin rubutu ba. Wannan zai taimaka wa duk wanda zai karanta samun sauƙin fahimtar saƙon da ake so a isar.
Salo: An yi rubutuncin cikin salo na jan hankali da nishaɗantar da mai karatu. Wannan wani muhimmin abu ne a cikin rubutun littafi, matuƙar ana son karɓuwarsa a wajen makaranta da manazarta.
Jerantawa: Kasancewar an yi fasalin littafin bisa jerantuwar babi-babi wani ƙarin armashi ne da jan hankali. Duk da babu wani babi na tsallakewa a labarin, amma duk da haka idan akwai wani babi da ya fi jan hankalin makaranci a cikin littafin, zai iya garzayawa don isa wurin da yake ya karanta. Haka nan a ƙarƙashin kowane babi, takan jero abubuwa da bayansu, waɗanda suka shafi wannan babin. Misali, idan aka je aka duba bayanin da ya shafi ‘gaskiya’. A ƙasanta ta jero ire-irenta kamar gaskiya a amana, gaskiya a nufi, gaskiya wajen yunƙuri da ƙuduri da wajen yin aiki. Duba shafi na 23. Haka ta yi a ƙarƙashin ‘soyayya’, wacce ta kasa ta kashi huɗu. Misalin, son Allah, so don Allah, so na ɗabi’a da sauransu. Hakan na cikin shafi na 25. Haka ta yi ta yi a sauran abubuwan da ta kawo a kowane babi. Don haka rubutun ba a zube yake kawai yadda za a sha wahalar nemo wani sashi a cikin littafin ba.
Bincike: Ko ba a faɗa ba an san cewa, aiki irin wannan yana matuƙar buƙatar zuzzurfan bincike kafin aiwatar da shi, musamman rubutu irin wannan da ya shafi addini, girke-girke, sirrin magunguna da kuma sana’o’i. Marubuciyar ta yi bincike a cikin wasu littattafan magabata, ta hanyar hira da masana, da kuma amfani da yanar gizo. Kamar yadda za a gani a shafukan 224 da 225 da kuma 226.
A taƙaice, kowane babi ka taɓo a cikin littafin wani fage ne muhimmi mai zaman kansa, wanda za a iya yin littafi sukutun guda a kansa. Misali, idan ka ɗauki babin da ke magana a kan girke-girke, tabbas an sha yin littattafai da ba za su ƙirgu ba, waɗanda suke koyar da girki. Haka nan sana’o’i. ballantana kuma uwa-uba a kan abin da ya shafi ibada.
Don haka ana iya cewa, wannan littafi shakundum ne wajen koyar da mata komai a rayuwarsu ta duniya. Don haka za mu iya cewa, mallakar wannan littafi wajibi ne ga kowacce musulma don sanin addininta da mu’amalarta.
Wannan a taƙaice ne, dangane da abin da wannan littafi ke ɗauke da shi. Sai idan an karanta, za a tarar ya fi haka.
Da fatan Allah ya ƙara wa wannan marubuciya basira da ƙwarin gwiwar ci gaba da yin irin waɗannan rubuce-rubucen don ƙaruwar al’umma.
Ibrahim Muhammad Indabawa,
Sakataren ƙungiyar Marubuta ta ƙasa (ANA),
Reshen Jihar Kano.
Mayu, 2025.
