NEDC ta miƙa makarantun Mega School ga gwamnatin Yobe

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu

Hukumar sake farfaɗo da Arewa maso Gabas (NEDC), ta ƙaddamar da sabbin makarantun Mega guda uku, waɗanda ta gina, tare da damƙa su ga gwamnatin Jihar Yobe, inda taron ya gudana a garin Potiskum, ranar Talata.

Bikin ƙaddamar da sabbin makarantun ya gudana a ƙarƙashin jagorancin Ministan Yanki, Uba Maigari Ahmadu, a harabar makarantar (Mega School) ta Ari-Kime 2, dake garin Potiskum, a Jihar Yobe.

Makarantun sun ƙunshi rukunin gine-ginen ajujuwa huɗu na benaye, masu ƙunshe da ajujuwan karatu 96 a fannin firamare da sakandare.

Sauran ɓangarorin da ginin makarantun suka ƙunsa su ne; ofishin gudanarwa, sito, gidajen ma’aikata, ɗakin shan-magani na gaggawa, da makamantan su.

Sa’ilin da da yake miƙa makarantun ga gwamnatin jihar, Minista Maigari ya yaba wa NEDC bisa ƙoƙari wajen gudanar da muhimman ayyukan ci gaban farfaɗo da yankin.

Ya ce, baya ga wannan, hukumar ta gina ƙarin wasu makarantu guda biyu a Gashu’a da Buni Yadi, a Jihar Yobe.

Ministan ya ce ya gamsu da ingancin waɗannan ayyukan da hukumar take aiwatarwa domin kawo gyara a yankin.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Mai Mala Buni, wanda sakataren gwamnatin jihar, Baba Mallam Wali, ya wakilta, inda ya godewa hukumar NEDC dangane da muhimman ayyukan ci gaba; daban-daban waɗanda ta aiwatar a faɗin jihar.

Ya ce ginin makarantun zai taimaka wajen magance cunkoson yara a azuzuwa, kuma zai inganta harkar ilimi a jihar.

By ukarofi