Gwamnatin Kano za ta hukunta gidan wasan da ya bar masu shigar banza da shaye-shaye

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ƙoƙarin ta na yaƙi da rashin ɗa’a tare da tsaftace yadda gidan wasanni da masu kiɗan DJ zasu gudanar da shagalin bikin sallah a Jihar Kano, Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba El-mustapha ta bayyana shirinta na saka ƙafar wando ɗaya da duk wani gidan wasa da ɗakunan taro ko masu kiɗan DJ da a ka samu da aikata yin rashin ɗa’a a yayin gudanar da bikin sallah a Jihar Kano. Hukumar ta kafa wani kwamiti na musamman da za su kewaya gidajen wasannin tare da ɗakunan taro a ranakun babbar sallah ƙarƙashin kulawar Alh. lawan Hamisu Ɗan Hassan daraktan dake lura da sashin fina-finai na hukumar.

Kwamitin wanda aikinsa shi ne saka ido a kan dukkannin gidajen wasannin da ɗakunan taro a Jihar Kano haɗi da masu kiɗan DJ zai tabbatar ba’a bawa masu shigar banza ko shaye-shaye damar shiga gidajen wasannin ba ko ɗakin taro haka kuma, hukumar ta hana haɗa maza da mata a guri ɗaya a yayin bikin na babbar sallar. Abba El-mustapha yace kwamitin zai rinƙa aiki ne a dare da rana ta cikin sirri tare da bayyana tun a rana ɗaya ga babbar sallah har zuwa lokacin da za’a kammala bikin sallar domin cimma nasarar aikin da a kasa a gaba.

Abba El-mustapha na ƙara yin gargaɗi da kakkausar murya ga masu gidajen wasanni da ɗakunan taro tare da masu sana’ar DJ dasu bi dokokin hukumar sau da ƙafa domin gujewa fushin doka.

A ƙarshe ya yi kira da iyaye da su cigaba da kula da tarbiyar ƴa ƴansu tare da addu’ar Allah yasa ayi bikin na sallah lafiya a gama lafiya.

By ukarofi