Tinubu ya taya ɗaliban Nijeriya uku murna bayan nasara a gasar ƙananan ɗalibai ta duniya

Spread the love

Shugaban Bola Tinubu ya taya ƴan matan nan uku da suka nuna bajinta a wata gasar ‘TeenEagle’ da aka yi a Birtaniya.

Ɗaliban sune Nafisa Abdullahi mai shekara 17 wadda ta haskaka a gasar Turanci yayin da Rukayya Muhammad Fema mai shekara 15 ta fi kowa hazaƙa a muhawara da Hadiza Kashim Kalli da ta lashe kyautar mafi fikira.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yaba wa matasan saboda bajintar da suka nuna a gasar .

Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa makarantu da sauran cibiyoyin karatu, inda ya ce irin waɗannan nasarori na bayyana yanayin ingancin da ilimi ke da shi a Nijeriya.

Ya bayyana ilimi a matsayin tushen duk wani cigaban ƙasa, lamarin da a cewarsa gwamnatinsa ke fifita ɓangaren tare da ganin ta kawar da duk wata matsala ta kuɗi da za ta hana ƴan ƙasar cigaba da karatu ta hanyar tsarin tallafin karatu na NELFUND, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Shugaban ƙasar ya kuma ƙarfafa wa Nafisa da Rukayya da Hadiza gwiwar mayar da hankali a karatu tare da yi masu fatan samun ƙarin nasarori a rayuwarsu.

By Babaji