DAGA JOHN D. WADA a Lafiya
Wata ƙungiya da ake kira NS-TA&G2 dake Jihar Nasarawa ta buƙaci akanta janar na gwamnatin Jihar Nasarawa Hon. Musa Ahmed Mohammed ya ajiye wannan muƙamin sa na mai sa ido a kuɗaɗen gwamnatin jihar idan yana sha’awar tsunduma cikin siyasa ko fitowa takarar kujerar gwamnan jihar.
Ƙunkiyar tayi kiran ne ga akanta janar ɗin ta bakin Lazarus Salaki a lokacin da suke zantawa da manema labarai a makon da ake ciki a birnin Lafiya babbar fadar gwamnatin jihar.
Yace kiran ya zama wajibi idan akayi la’akari da yadda duk da wata umurni na musamman da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule yayi wa duka maƙarraban sa dake riƙe da mahimman muƙamai cewa su ajiye muƙamin nasu idan suna son shiga siyasa dumu-dumu amma sai kawo yanzu a cewar sa tuni ƙungiyar ta gano cewa akanta janar ɗin Hon. Musa Ahmed Mohammed yana cigaba da bijire wa umurnin gwamnan inda yake cigaba da gudanar da harkokin siyasar sa musamman ta wata ƙungiyar yaƙin neman zaɓen sa a matsayin gwamnan jihar a 2027 wadda wasu na kusa dashi suka kafa da ake kira Barade Network a turance.
Lazarus Salaki ya bayyana takaicin ƙungiyar da al’ummar jihar baki ɗaya dangane da yadda maimakon akanta janar ɗin ya bada fifiko ga mahimman aikin nasa na sa ido a harkokin kuɗaɗen gwamnatin jihar sai yake cigaba da gudanar da harkokin sa na siyasar ba tare da yin la’akari da illolin hakan ga gwamnatin Abdullahi Sule da tattalin arzikin jihar ba.
Lazarus ya cigaba da bayyana cewa” muna bayyana takaicin mu da rashin jin daɗin mu ne a madadin babbar jam’iyyar mu mai mulki APC musamman dangane da yadda akanta janar na jihar nan Hon. Musa Ahmed Mohammed da ake wa lakabi da Barade a yanzu haka ake zargi da tsunduma cikin siyasa ta wasu hanyoyi da suka hada da gudanar da tarurrukan siyasa na sirri da ɗaukan nauyin fostocin hotunan sa na fitowa takarar kujerar gwamnan jihar a inuwar APC a 2027 da sauran su.
Tabbas idan wannan zargi gaskiya ne to basu dace da mutumin dake riƙe da wannan mahimmin muƙami na tabbatar da inganci da adalci a dukiyar gwamnati ba.
Sanin kowa ne cewa ofishin akanta janar ofishi ne na kowa dake buƙatar ƙwarewa da rashin siyasa don hakan ka iya jawo wa APC baƙin jini da zarge-zarge musamman daga jam’iyyun adawa da sauran su.
Amma idan shi (Barade) yana sha’awar kujerar siyasa abinda yakamata yayi a hukumance a yanzu kawai shine ya ajiye wannan muƙamin nasa domin bin umurnin doka.”
Ƙunkiyar har ila yau tayi amfani da damar inda tayi misali da wasu jiga-jigan jihar da ke riƙe da manyan muƙaman gwamnatin jihar a yanzu da tace suke bin umurnin gwamnan ta yin nesa da siyasa a yanzu cewa ciki har da babban sakataren gwamnatin jihar Barr. Labaran Magaji da sauran su.
A cewar ƙungiyar waɗannan mutane duk da suna samun gayyata da tayin fitowa su shiga harkar siyasar a yanzu amma suna guje wa hakan a kullum don kare mutuncin su da ta gwamnatin jihar da ma shi kansa uban gidan nasu gwamna Abdullahi Sule saboda haka dole ne shima akanta janar ya bi sawun su.
A ƙarshe sai ƙungiyar ta bakin Lazarus Salaki ta jawo hankalin ire-iren su akanta janar ɗin da ke bijirewa umurnin gwamnan cewa su tuna abinda ya faru a Jihar Ribas tsakanin gwamna Fubara da uban gidan sa na siyasa wato Nyesom Wike da hakan ya jawo wa jihar dokar ta ɓaci, saboda haka dole ne masu riƙe da manyan muƙamai a jihar su sani cewa irin bala’in Ribas ɗin ya kan samo asali ne sakamakon rashin kishin ƙasa na asali tare da siyasar son zujiya da makamantan su.
Don haka a cewar sa bai dace a sa hakan ya faru a jihar ta Nasarawa ba inda ya ƙara da cewa “Allah ya albarkace mu da gwamna da ke gudanar da shugabanci na adalci da riƙon amana da ke kuma cigaba da aiwatar da ɗimbin ayyukan cigaba wato mai girma gwamna Abdullahi Sule.
” Saboda haka a nan muna kira ga duka masu riƙe da muƙaman gwamnati a siyasance musamman akanta janar na jiha su cigaba da bai wa gwamnan cikakken goyon baya su guji siyasa a yanzu sai lokaci yayi kamar yadda gwamnan ya umurce su kwanakin baya don cigaban al’ummar mu baki ɗaya.
“Sa’anan mu a namu ɓangaren a ƙungiyar NS-TA&G2 muna jaddada aniyar mu na tabbatar da adalci da shugabanci na gari da kuma aiki da shari’a da dokoki don mu na kowa ne kuma kowa namu ne.” Inji shi.
