Wasiƙar da Xi ya rubuta ga mahaifinsa

Daga CMG HAUSA

Yau ranar 19 ga watan Yuni, ranar mahaifa ce ta ƙasa da ƙasa, bari mu yi muku bayani kan labarin da ya faru tsakanin shugaban ƙasar Sin Xi Jinping da mahaifinsa Xi Zhongxun.

Haƙiƙa Xi Zhongxun ya kawo babban tasiri ga ɗansa shugaba Xi a ɓangarorin rayuwa da aiki, ana iya gano lamarin daga wata wasiƙar da ya rubuta ga mahaifinsa.

Ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2001, ranar murnar cika shekaru 88 na haihuwar Xi Zhongxun, inda ɗaukacin iyalan Xi suka taru a gidansa domin tayashi murna, amma Xi Jinping wanda ya kasance shugaban lardin Fujian a wancan lokacin, bai koma gida ba, sakamakon aiki, don haka ya rubuta wata wasiƙa ga mahaifinsa.

A cikin wasiƙar da ya rubata, Xi ya bayyana cewa, ya koyi halayya na gari daga mahaifinsa, yana mai cewa, “Kai kamar bijimi mai ƙwazo ne, dake aiki ba dare ba rana domin bauta wa al’ummar ƙasa, lamarin da ya ƙara ƙarfafa mini gwiwa, har na ƙudiri aniyyar bauta wa al’ummun Sinawa a duk tsawon rayuwata.”

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa